Trump: A Karo na 4, Majalisar Amurka Ta Sake Kuri'a kan Yaƙi da Iran
- Majalisar dattawan Amurka ta sake zama a kan kudirin hana Shugaban ƙasar, Donald Trump ci gaba da yaƙi da Iran karo na huɗu
- Sai dai ƙuri’ar ta rabu tsakanin jam’iyyun siyasa, inda mafi yawan ‘yan Republican suka ƙi amincewa da kudirin
- Masu goyon baya sun ce Trump ya wuce makaɗi da rawa a fuskar kundin tsarin mulki, amma magoya bayansa sun kare matakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
USA – Majalisar dattawan Amurka ta sake yin watsi da wani kudiri da ke neman takaita ikon Shugaban ƙasar, Donald Trump, na ci gaba da yaƙi da Iran.
Wannan shi ne karo na huɗu da ake ƙoƙarin amincewa da irin wannan kudiri domin saka masa takunkumi kan yaƙin, amma bai samu nasara ba.

Kara karanta wannan
Kasar Rasha ta kawo mafita ga shirin nukiliyar Iran, abin bai yi wa Amurka dadi ba

Source: Facebook
Al-Jazeera ta wallafa cewa an yi wannan ƙuri’a ne bayan Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta na makonni biyu a makon da ya gabata.
Majalisar Amurka ta zauna kan yakin Iran
NBC News wallafa cewa duk da haka, tattaunawar da aka yi a Islamabad ba ta kai ga cimma yarjejeniya mai ɗorewa ba, duk da cewa bangarorin biyu sun nuna shirinsu na sake komawa tattaunawa.
Kafin tsagaita wutar, Trump ya sha yin barazanar kai hare-hare kan muhimman wuraren fararen hula a kasar Iran yayin da yaƙin ke ƙara zafi.
Wata barazana da ya yi a ranar 7 ga Afrilu 2026 cewa duk wata al’umma za ta mutu cikin dare guda ta janyo ƙarin kira daga ‘yan majalisa da su dakile ikon shugaban ƙasar wajen yanke shawarar yaƙi.
Yadda majalisar Amurka ta tashi
Kuri’ar ta ƙare da sakamakon 47 zuwa 52, inda ɗan Republican guda, Rand Paul, ya goyi bayan kudirin, yayin da ɗan Democrat guda, John Fetterman, ya ƙi shi.

Source: Getty Images
Masu goyon bayan kudirin sun dage cewa Trump ya keta kundin tsarin mulkin Amurka lokacin da ya fara yaƙi tare da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa Majalisa ce ke da ikon ayyana yaƙi, sai dai shugaban ƙasa na iya ɗaukar mataki kai tsaye idan akwai gaggawar kare kai.
Sai dai gwamnatin Trump ta kare kanta da cewa matakan Iran tun bayan juyin juya halin 1979 sun zama barazana kai tsaye ga kasar Amurka.
Kafin ƙuri’ar, Sanata Chris Murphy ya soki yaƙin, yana mai cewa an tafiyar da shi cikin rudani kuma bai cimma manufofin gwamnati ba.
Sai dai Sanata Jim Risch ya kare Trump, yana cewa shugaban ƙasa yana da cikakken iko da kuma alhakin kare al’ummar Amurka.
Amurka da Iran za su tattauna
A baya, mun wallafa cewa Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya yi magana da Shugaba Donald Trump ta wayar salula kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.
Fadar Sarkin Qatar ta tabbatar da tattaunawar shugabannin kasashen biyu, inda ta jero muhimman batutuwan da suka tabo da suka shafi yakin da Amurka da Isra'ila suka takalo.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin sake shirya tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a karo na biyu a birnin Islamabad da ke Pakistan domin samar da sulhu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

