Zaben fidda gwanin PDP: Jerin wadanda za su yi takara a majalisar jiha da ta tarayya a karkashin PDP a Gombe

Zaben fidda gwanin PDP: Jerin wadanda za su yi takara a majalisar jiha da ta tarayya a karkashin PDP a Gombe

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe ta kammala zaben fidda yan takararta na majalisar dokokin jiha da na wakilai a ranar Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto cewa mutum shida sun bayyana a matsayin yan takarar kujerar yan majalisar wakilai, yayin da 24 suka tabbata a masu takarar kujerar yan majalisar jiha.

Zaben fidda gwanin PDP: Jerin wadanda za su yi takara a majalisar jiha da ta tarayya a karkashin PDP a Gombe
Zaben fidda gwanin PDP: Jerin wadanda za su yi takara a majalisar jiha da ta tarayya a karkashin PDP a Gombe Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ga jerin sunayen yan takarar kamar yadda jam’iyyar ta saki a jihar Gombe a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu:

Majalisar dokokin jiha

Karamar hukumar Akko

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Abdullahi Gaddafi - Akko ta tsakiya

2. Umar Kalajanga - Akko ta arewa

3. Alhaji Adamu Kashere - Akko ta yamma

Kara karanta wannan

2023: 'Yan kwamiti sun haramtawa tsohon Sanatan PDP shiga zaben neman Gwamna a APC

Karamar hukumar Balanga

1. Meriji Majoro - Balanga ta kudu

2. Saratu Jauro - Balanga ta arewa

Karamar hukumar Billiri

1. Yakubu Ladollis - Billiri ta gabas

2. Nimrod Yari - Billiri ta yamma

Karamar hukumar Dukku

1. Zakariyya Sa’idu - Dukku ta kudu

2. Abdulrahman Zaune - Dukku ta arewa

Karamar hukumar Funakaye

1. Mohammed Buba - Funakaye ta arewa

2. Abubakar Adamu - Funakaye ta kudu

Karamar hukumar Gombe

1. Ahmed Abubakar - Gombe ta arewa

2. Ismail Usmandodo - Gombe ta kudu

Karamar hukumar Kaltungo

1. Gabriel Galadima - Kaltungo ta yamma

2. Hassan Reuben - Kaltungo ta gabas

Karamar hukumar Kwami

1. Adamu Rilwanu - Kwami ta yamma

2. Ahmad Abubakar - Kwami ta gabas

Karamar hukumar Nafada

1. Haji Baba - Nafada ta arewa

2. Ibrahim Musa - Nafada ta kudu

Karamar hukumar Shongom

1. Zubairu Ayala - Shongom

2. Markus Samuel - Pero Chonge

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari ya nada sabon Shugaban hukumar lissafi da kididdiga

Karamar hukumar Yamaltu Deba

1. Salisu Lano - Deba

2. Kabiru Wade - Yamaltu ta gabas

3. Samaila Garba - Yamaltu ta yamma

Yan majalisar wakilai

1. Dukku/Nafaɗa - El-Rasheed Abdullahi

2. Gombe/Kwami/Funakaye - Hon Yaya-Bauchi Tongo

3. Akko - Aishatu Ahmad

4. Yamaltu Deba - Inuwa Garba

5. Billiri/Balanga - Ali Isa

6. Kaltungo/Shongom - Obed Shehu

A gaba daya, yan takara mata uku ne kawai aka zaba cikin masu takararar kujerar 30 a zabukan biyu, biyu na majalisar dokokin jaha yayin da dayar ta mallaki tikitin majalisar wakilai a zaben fidda gwanin.

2023: Sheikh Ibrahim Khalil ya tabbata dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADC

A wani labari na daban, fitaccen malamain nan na Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, ya zama dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jam’iyyar Africa Democratic Congress (ADC), Solacebace ta rahoto.

An tattaro cewa Sheikh Khalil wanda ya zama dan takarar jam’iyyar bayan ya bayyana bai da abokin hamayya a wani taro da aka gudanar a ranar Lahadi, zai yi fafutukar babbar kujerar jihar ne tare da yan takarar sauran jam’iyyun siyasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya nada Dr Tutuwa Adamu matsayin shugabar FIIRO

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng