Gwamna da Sarki a Arewa sun ba takarar Osinbajo kwarin gwiwa, su na goyon bayansa a 2023

Gwamna da Sarki a Arewa sun ba takarar Osinbajo kwarin gwiwa, su na goyon bayansa a 2023

  • A jiya Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara domin ya gaida Mai martaba Sarkin Gombe a fadarsa
  • Mataimakin shugaban kasar ya je ne Gombe domin samun kuri’un ‘Yan APC a zaben fitar da gwani
  • Alhaji Abubakar Shehu Abubakar ya yabi Osinbajo saboda halayen kirki da kuma kan-kan da kansa

Gombe - Mai girma Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya nuna goyon bayansa ga takarar da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yake son yi.

Hukumar dillacin labarai ta fitar da rahoto cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna hakan a sa'ilin da Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci fadar Sarkin Gombe.

A ranar Litinin, 9 ga watan Mayu 2022, Osinbajo ya kai ziyara ga Alhaji Abubakar Shehu Abubakar yayin da ya je ganawa da ‘ya ‘yan jam'iyyar APC a jiharsa.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Da Gwamnan na Gombe yake jawabi a fadar Mai martaban, an ji ya na yabon Yemi Osinbajo, har yana cewa yana sa rai zai zama shugaban Najeriya.

Inuwa Yahaya yake cewa yana sa ran idan Farfesa Osinbajo ya karbi mulki, za a samu cigaba, sannan zai inganta halin da al’ummar kasar nan ke ciki.

A cewar Inuwa Yahaya, babu tantama cewa Osinbajo ya fi kowa cancanta ya zama shugaban kasa. Wannan rahoto ya fito a jaridar nan ta Daily Nigerian.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Osinbajo
Yemi Osinbajo wajen bikin sallah a Kano Hoto: @professoryemiosinbajo
Asali: Facebook

Jawabin Gwamna Inuwa Yahaya

“Mu masu kishin-kasa ne, mu na so kasar nan ta cigaba, mu kai zuwa ga matakin da ake buri.”
“Zan iya fada da babbar murya cewa mutanen nan da ka ke gani da kayan sarauta, da na bangaren gwamnati, da taron da ke waje, su na so ka cin ma burinka na zama shugaban Najeriya idan Allah ya so.”

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Inuwa Yahaya ya lamuncewa Kayode Fayemi don ya gaji shugaba Buhari

“Gombe gidan mataimakin shugaban kasa ne saboda wasu dalilai da-dama; duba da yadda abubuwa su ke, kai ka fi dacewa da kujerar.”

- Inuwa Yahaya

Osinbajo ya taka rawar gani - Sarki

Da yake na shi bayanin, Mai martaba Shehu Abubakar ya bayyana irin nasarorin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu a sanadiyyar Farfesa Osinbajo.

Sarkin ya yi wa Osinbajo fatan alheri, ganin yana da abin da zai nuna saboda irin sanin aikinsa da kyawawan halinsa, tare da sanin kimar jama’a da yake da shi.

Gwamnoni na ta lissafin 2023

An samu labari cewa wasu Gwamnonin da ke shirin barin gadon mulki sun fara bayyanawa Duniya wadanda za su rikewa hannu a zaben da za ayi a 2023.

A karshen makon jiya ne Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi abin da da yawa ba su yi, ya zabi mataimakinsa, Nasiru Gawuna a matsayin magajinsa a APC.

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi ya yi maza ya yi karin-haske, ya karyata jita-jitar goyon bayan Osinbajo

Asali: Legit.ng

Online view pixel