FCDO: Dalilan da Suka Sa Jami'an Birtaniya Halartar Taron ADC a Abuja

FCDO: Dalilan da Suka Sa Jami'an Birtaniya Halartar Taron ADC a Abuja

  • Birtaniya ta kare matakin da ta dauka ba barin jami'anta su halarci a taron jam’iyyar ADC da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja
  • Hukumar FCDO ta ce irin wannan mu’amala na cikin aikin diflomasiyya na yau da kullum da jami'anta ke yi lokaci zuwa lokaci
  • A nata bangaren, China ta yi magana game da zargin jami'anta sun halarci babban taron ƴan hamayya a Abuja

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja– Gwamnatin Birtaniya ta kare halartar wasu jami’anta a babban taron jam’iyyar ADC, tana mai cewa irin wannan mu’amala wani bangare ne na aikin diflomasiyya na yau da kullum.

A lokacin taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja ranar Talata, 14 ga watan Afrilu , 2027, shugabannin ADC sun bayyana cewa tawaga mai mutane uku daga ofishin jakadancin Birtaniya ta halarci taron.

Kara karanta wannan

Wutar rikici ta fara tashi a jam'iyyar APC, Yilwatda ya gargadi tsafaffin ƴan PDP

Jami'an Birtaniya sun halarci taron ADC
Bolaji Abdullahi, Sakataren yaɗa labaran ADC da alamar jam'iyya Hoto: Bolaji Abdullahi/ADC Party
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa jam’iyyar ta ce Thomas Samson, sakataren siyasa na ofishin jakadancin, ne ya jagoranci tawagar, tare da Damilola Oyedele, ma’aikaciyar Najeriya a ofishin.

ADC ta ce ƴan China sun halarci taronta

Jaridar Leadership ta wallafa cewa jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa jakadan ƙasar China a Najeriya, Yu Dunhai, ya halarci taron da ta shirya.

Ofishin jakadancin China ya bayyana cewa babu jakadansa ko wani jami’in diflomasiyya na kasar da ya je taron.

Ya ce wani mutumin Asiya da aka gani a wajen taron, wanda wasu jiga-jigan ADC suka ce jakadan China ne, ba a san shi ba a ofishin jakadancin.

Taron ADC: Birtaniya na karfafa tsarin dimokuraɗiyya

Sai dai ofishin Birtaniya na FCDO ya bayyana cewa jami’anta kan halarci irin wadannan taruka na siyasa da na farar hula lokaci zuwa lokaci.

A cewar kakakin FCDO, halartar irin wadannan abubuwa abu ne na yau da kullum, domin ofishin jakadancin na hulɗa da bangarori daban-daban na siyasa.

Kara karanta wannan

APC a Adamawa ta rikice, mai neman takarar gwamna ya fice daga jam'iyya

Birtaniya ta ce zuwa taron ADC na daga cikin abin da jami'anta ke yi
Wasu daga cikin jiga-jigan ADC a taronsu na farko bayan farfaɗo da jam'iyya Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Ofishin ya ce:

“Jami’an ofishin jakadancin Birtaniya, kamar sauran ofisoshin kasashen duniya, ana gayyatarsu kuma suna halartar taruka daban-daban, ciki har da na jam’iyyun siyasa."

Ya kara da cewa halartar irin wadannan taruka na nuna kudirin gwamnatin Birtaniya na tallafawa tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Haka kuma, FCDO ya bayyana cewa Birtaniya na goyon bayan zaben gaskiya, kuma a cikin lumana ta hanyar hadin gwiwa wajen inganta tsarin mulki da sahihancin zabe.

Duk da cewa ofisoshin jakadanci kan yi hulɗa da bangarori daban-daban na siyasa, daga ciki har da ‘yan adawa, ba kasafai ake ganin jakadu na halartar manyan tarukan jam’iyyun siyasa ba ko a gabatar da su ga mahalarta.

A halin yanzu, jam’iyyar ADC na kokarin zama babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, inda take jawo tsofaffin jiga-jigan APC da sauran ‘yan siyasa daga bangarori daban-daban.

Atiku ya magantu kan takara a ADC

A baya, mun wallafa cewa tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce jam’iyyar ADC ta shirya tunkarar zaben 2027 mai zuwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya 'gano' halin da APC ke ciki, ya fadi hadin da zai kai Tinubu ƙasa a 2027

Ya bayyana cewa zaben 2027 zai zama karo na ƙarshe da zai nemi shugabancin Najeriya ganin cewa shekaru sun cin masa saboda haka zai hakura.

Tsohon mataimakin shugaban, Atiku Abubakar ya ce ADC na duba amfani hanya ɗaya ko biyu wajen fitar da wanda zai kara da APC a 2027 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng