N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai

N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai

  • Sanata Danjuma Goje ya baiwa sama da mutane 2,000 a mazabarsa dake jihar Gombe tallafin fara sana'o'i
  • Tsohon gwamnan jihar ya raba makudan kudade ga wadanda suka ci gajiyar tallafin domin su fara sana’ar da suka iya
  • Sanata Goje ya yi amfani da wannan damar wajen baiwa gwamnatin tarayya shawara domin shawo kan matsalar rashin aikin yi a kasar nan

Matasa da mata 2,200 a Gombe ne Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa, Sanata Danjuma Goje ya ba tallafin sana'a.

Legit.ng ta samo cewa, Goje, wanda tsohon gwamnan jihar Gombe ne ya raba musu makudan kudade a matsayin jarin fara kasuwancin da suka iya a ranar Litinin, 29 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Daga cikin mutane 2,200 da suka ci gajiyar shirin karfafawar ta Sanata Goje, 1000 matasa maza ne yayin da 1,200 kuma mata ne, wadanda dukkansu sun fito ne daga kananan hukumomin Yamaltu-Deba da Akko.

N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai
N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Ko da yake ba a fayyace gudunmawar ta kudaden da aka bai wa mata 1,200 ba, kowanne daga cikin matasan ya samu Naira 30,000, wanda jumillarsu ya kai Naira miliyan 30.

Matasa 1,000 ne aka zaba kana aka horar da su sana’o’i daban-daban daga Hukumar Kula da Ayyukan yi ta kasa (NDE), don samun dogaro da kai.

Manufar ba da tallafin

Da yake jawabi jim kadan bayan gabatar da jarin ga matasa da mata, Goje ya bukace su da su yi amfani da kudin wajen abubuwan da suka dace, ya kara da cewa hakan ya yi daidai da manufarsa ta rage radadin da jama’a ke ciki.

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

A cewar Goje, tun da farko ya tallafa wa mutane da kayan abinci, da kuma kayayyakin sana'a da suka hada da keken dinki da na’urorin samar da wutar lantarki domin bunkasa sana’arsu.

Sanatan ya samu wakilcin hadiminsa na musamman Barr. Saidu Kumo, ya kuma nuna damuwarsa kan karuwar rashin aikin yi tsakanin matasa a jihar, tare da illar da ke tattare da al’umma.

A kalamansa:

“Wannan shiri an yi shi ne da nufin kawar da talauci da kuma karfafa wa matasanmu na Gombe ta tsakiya da basu damar samun walwala.
“Wannan al’ada ce ta siyasar Sanata Goje wajen tallafawa mutane dama tun dawowar dimokuradiyyar nan don samun aikin yi kai tsaye ko a fakaice.”

Barr Kumo ya ce manufar ba da jarin fara sana'ar ita ce karfafa dogaro da kai tare da kawar da talauci da rashin aikin yi da nufin bunkasa tattalin arzikin jihar.

Ya tabbatar da cewa shirin wani bangare ne na aikin mazabar Sanata, inda ya ce:

Kara karanta wannan

Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya

“Sanatan ya yi abubuwa da yawa, yana gina makarantu, masallatai, asibitoci, samar da motocin bas, motocin daukar marasa lafiya, da aiwatar da ayyukan samar da wutar lantarki a yankunan karkara.”

An zabo mu ne daga mazabun Akko da Yamaltu Deba

A wata tattaunawar wayan talho tsakanin wakilin Legit.ng Hausa da Abdulazeez Hassan; daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, ya bayyana yadda aka zagulo wadanda suka mori shirin.

A cewarsa:

"A baya an yi na mata, an zabi 1200, an basu N30000, yanzu kuma na maza aka yi mu ma an bamu N3000 kowannenmu. Muna yiwa sanatanmu fatan alheri, sannan muna godiya da wannan gudunmawa."

Rikcin Goje da Inuwa: Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltan Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje ya nemi Sufeto Janar na 'yan sanda, Alkali Baba da babban Atoni Janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami da su binciki harin da aka kai masa.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya rafke matar aure da tabarya, ya halakata a gaban yaranta a Kano

Goje ya yi zargin cewa harin da aka kai masa a Gombe yunkuri ne na hallaka shi da hadiminsa, Adamu Manga.

Ya yi zargin cewa dogarin gwamna Inuwa Yahaya, Zulaidaini Abba da shugaban tsaron gwamnan, Sani Bajoga sune manyan wadanda ake zargi, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel