Za a Samu Barkewar Cututtuka a Kaduna, Kogi da Jihohi 8, Gwamnati Ta Yi Bayani
- Hukumar NCDC ta gargaɗi ƴan Najeriya game da bullar cutar gudawa da sauran cututtuka sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi hasashe a 2026
- NCDC ta yi hasashen cewa za a samu bullar cututtukan a Kaduna, Kogi da jihohi takwas, wanda ya zama wajibi mazauna jihohin su dauki mataki
- Shugaba Bola Tinubu dai ya jaddada cewa gwamnatinsa na ba da fifiko ga magance ambaliya don tabbatar da wadatar abinci da tsaron rayuka
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC), ta fitar da gargaɗin gaggawa ga al'umma game da yiwuwar bullar cutar kwalara da sauran cututtukan dake da alaƙa da ambaliyar ruwa.
Wannan gargaɗi na zuwa ne biyo bayan hasashen da ma'aikatar muhalli da hukumar NiMet suka yi, na cewa za a fuskanci ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya tsakanin ranar 13 zuwa 17 ga watan Afrilu, 2026.

Source: Twitter
Za a samu barkewar cututtuka a jihohi 10
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa Gwamnatin tarayya ta lissafa jihohin da ke cikin babban haɗarin barkewar cututtuka kamar haka:
A cikin shawarwarin da ta bayar, NCDC ta yi gargaɗin cewa ambaliyar na iya haifar da cututtuka kamar kwalara da gudawa, sannan za a iya samun ƙaruwar cutar zazzabin cizon sauro.
Shawararin NCDC ga 'yan Najeriya
Haka kuma, ambaliyar na iya janyo raunuka ga mutane, gurbata hanyoyin shan ruwa, da kuma dakile ayyukan samar da lafiya a asibitoci.
Domin tabbatar da jama'a sun shirya, NCDC ta ba da shawarwari kamar haka:
- Shan ruwan da aka tafasa ko aka sanya masa maganin kashe ƙwayoyin cuta (chlorine).
- Wanke hannu akai-akai da sabulu da ruwa mai tsafta.
- Amfani da gidan sauro domin guje wa kamuwa da zazzabin ciwon sauro.
- Duk wanda ya ga alamun gudawa, amai, ko zazzabi ya gaggauta zuwa asibiti mafi kusa.

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya 'gano' halin da APC ke ciki, ya fadi hadin da zai kai Tinubu ƙasa a 2027
Hukumar NCDC ta ce tana aiki kafa-da-kafa da gwamnatocin jihohi domin ƙarfafa sa ido da kuma shirye-shiryen gaggawa don rage radadin duk wata cuta da za ta iya ɓarkewa sakamakon wannan ambaliya.
Tinubu ya yi maganganu kan ambaliyar ruwa
A nasa jawabin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ambaliyar ruwa na ɗaya daga cikin manyan barazana ga ci gaban Najeriya, wadatar abinci, da tsaron rayuka, in ji rahoton The Guardian.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa Najeriya ta daɗe tana fuskantar wannan matsala tun a shekarar 2012, wanda hakan ya hada da ambaliyar da ta taba afkuwa a Maiduguri, jihar Borno a shekarar da ta gabata.
Shugaban ya jaddada cewa, ɗaya daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa shi ne tabbatar da wadatar abinci, kuma hakan ba zai yiwu ba sai idan an magance matsalar ambaliya.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kaddamar da ayyukan magance ambaliya a sassan ƙasar, musamman a jihohin da abin ya fi shafa kamar Adamawa, Taraba, Benue, Kogi, Delta, da Rivers.
Jihohi 33 za su fuskanci ambaliyar ruwa
A wani labari, mun ruwaito cewa, Ma'aikatar albarkatun ruwa ta sanar da cewa garuruwa 14,118 a ƙananan hukumomi 266 za su fuskanci barazanar ambaliya.
Jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya Abuja ne aka yi hasashen cewa ambaliyar za ta shafa tsakanin watan Afrilu zuwa Nuwamba, 2026.
Manyan birane kamar Legas, Kano, Abuja, da Kaduna za su fuskanci ambaliya mai tsanani sakamakon toshewar magudanun ruwa a jihohinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

