Gwamnatin tarayyar Najeriya
Wata gobara ta barke a wata kasuwa dake cikin jihar Legas. Gobaran ta kone shaguna 62 kurmus tare da wani gida dake kusa da kasuwar mai dauke da dakuna 24.
Gwamnatin jihar Ekiti ta ware makudan kudade sama biliyan daya cikin kasafin kudin shekarar 2021 na jihar domin karfafa aikin hukumar tsaro ta jihar; Amotekun.
Majalisar dattijan Najeriya ta zargi ma'aikatar albarkatun man fetur da kashe N98.4m ba kan ka'idar gwamnati ba. An kashe kudin ne wajen buga takardun kalanda
Wani mutum ya kai kudin fansar 'yan uwansa da a ka yi garkuwa dasu shi ma an hada dashi. 'Yan uwan mutumin sun bayyana zaman dardar da suke yi a yankin nasu.
Rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara ta cafke wasu mutane 4 da bindigogi. Ana zargin mutanen da kisan wani bafulatani tare da kwace shanunsa. An kwato shanu 200.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jami'an diflomasiyyar kasashen waje su ma dole ne su yi rajistar katin dan kasa (NIN) matukar zasu kai shekara 2 a Najeriya.
'Yan kasuwa 18 da aka sace sun samu an sake su jiya Asabar bayan biyan kudin fansa. Kungiyar 'yan kasuwan arewa sun tabbatar da sakin su a yammacin jiya Asabar.
Gwamnan jihar Borno, ya bayyana cewa ba muslumai da bakaken fata kadai ne a cikin 'yan Boko Haram ba. Gwamnan yace akwai Kiristoci da fararen fata a cikinsu.
Rikici ya barke tsakanin wasu jigogin siyasar jihar Kaduna (Uba Sani da Yusu Zailani)kan harin kujerar gwamna da kujerar sanata a yankin Kaduna ta tsakiya.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari