Dangote ya kammala aikin titin kankare mafi tsayi na farko a Najeriya
- Kamfanin Dangote ya yi wata hanyar kankare da babu irin ta a fadin Najieriya baki daya
- Kamfanin ya kammala aikin titin da ya kai tsawon kilomita 43 a Obajana
- Sarakunan gargajiya da mazauna yankin sun jinjinawa Dangote kan wannan katafaren aikin
Rukunin kamfanonin Dangote ya kammala shimfida mafi tsawon titin kankare a Najeriya a jihar Kogi. Ita ce irinta ta farko, a cewar manyan injiniyoyi, Reuben Abati ya ruwaito.
Masu motoci sun bayyana hanyar Obajana-Kabba mai tsawon kilomita 43, wanda kamfanin Dangote Industries Limited (DIL) ya gina, a matsayin babbar hanyar kasar da ta fi dacewa wajen taimaka wa matafiya tsakanin Arewa da Kudu.
Daraktan Ayyuka, Olatunbosun Kalejaiye ya ce ya yi matukar farin ciki da aka gabatar da aikin 'Corporate Social Responsibility (CSR)' don amfanin 'yan Najeriya.
KU KARANTA: Tsohon shugaban kwastam da wani sun mayar da N8bn asusun gwamnati
Ya kara da cewa yayin da aka gama tsayayyar shimfidar hanyar, kamfanin yana gyara gefen hanyar.
Injiniyan aikin Samuel Obosi ya ce hanyar, mai hannu biyu za ta kasance mai karko kuma ba za ta kasance cikin sauki ga ramuka da gyara ba, kamar hanyar kwalta.
“Na gode wa Allah, hanya ce ta kankare. Tana iya jure duk wata motar daukar nauyi,” Alhaji Lamidi Sikiru, wani direba ya ce.
Wani memba na kungiyar kwadago ta Direbobi ta Kasa (NURTW), John Moses, ya ce kasuwancin tasi na ta bunkasa, idan aka kwatanta da lokacin da hanyar ke cikin mawuyacin hali tare da ramuka kuma masu ababen hawa suka kaurace mata.
Wani shugaban al’umma a masarautar Apa Bunu kuma mai magana da yawun Sam Omosayil ya ce hanyar ta jawo ‘yan kasuwa da dama zuwa yankin.
Sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma sun yaba wa Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote.
KU KARANTA: Gobara ta lashe shaguna 62 a Legas
“Dangote dan mu ne. Zamu kare babbar hajarsa sa da kuma katafariyar hanyar kankare. Ina farin ciki da faruwar hakan a rayuwata da masarautata. Wannan babbar dama ce a gare mu da kuma tsararraki masu zuwa,” inji shi.
A wani labarin, Kamfanin takin zamani na Dangote ya gina katafariyar dakin karatun zamani da miliyoyin naira na zamani tare da mika shi ga hukumar kula da ilimin bai-daya ta jihar Legas, Jaridar The Punch ta ruwaito.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Lahadi ta ce, gudummawar makarantar na da nufin samar wa al’ummar Abejoye da ke yankin Ibeju-Lekki na Legas ingantaccen ilimi ta hanyar samar da kayayyakin koyarwa da kuma yanayi mai kyau.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng