Ana Zargin Tinubu ba Shi da Lafiya da Ya Yi Wasu Maganganu a Abuja

Ana Zargin Tinubu ba Shi da Lafiya da Ya Yi Wasu Maganganu a Abuja

  • Hadimin Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo, ya ce uzurin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar na guje wa halartar wasu taron yaƙin neman zaɓe alama ce ta cewa ba shi da lafiya
  • Yayin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC a ranar Laraba, shugaban ya shaida wa taron cewa ba zai riƙa zuwa kowane wurin yaƙin neman zaɓe ba
  • Shugaba Tinubu ya shaida wa kwamitin yaƙin neman zaɓen ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yari cewa ba zai sami damar zuwa dukkan jihohi da ƙananan hukumomi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre na kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hadimin Atiku, Kenneth Okonkwo, ya bayyana cewa aniyar Shugaba Bola Tinubu na guje wa halartar taron yaƙin neman zaɓe na nuni da cewa ba shi da lafiya da zai iya gudanar da aikin.

Kara karanta wannan

An samu akasi harshen Tinubu ya suɓuce, ya tafka kuskure a tsakiyar jama'a a Abuja

A lokacin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam'iyyar APC a ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya shaida wa taron cewa ba zai samu damar kewaya dukkan jihohi da ƙananan hukumomi ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa Tinubu ya bayyana cewa nauyin da ke kansa na shugabancin ƙasa yana buƙatar kulawa ta musamman, don haka zai bar sauran mambobin kwamitin su gudanar da yaƙin neman zaɓe a jihohi da ƙananan hukumomi.

A bayanin da ya yi, Tinubu ya ce:

"Najeriya na buƙatar kulawa sosai a yanzu fiye da kowane lokaci. Aikin wannan ofis din ba zai tsaya ba. Duk da haka, zan samu lokacin magana kai tsaye da 'yan Najeriya, koda yake ku ne za ku jagoranci yaƙin neman zaɓe a jihohi da ƙananan hukumomi. Don haka za ku yi min afuwa na rashin zuwa ko'ina tare da ku."

Zargin Tinubu ba lafiya

A raddin da ya fitar a cikin wata sanarwa, Okonkwo, wanda yake ɗaya daga cikin masu magana da yawun Atiku Abubakar, ya ce Tinubu ba shi da ƙarfin jiki na gudanar da gagarumin aikin yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Tinubu ba zai iya zuwa kamfe a wasu jihohin Najeriya ba

Ya bukaci shugaban ƙasar da ya yi murabus bisa wannan dalili, yayin da yake kiran 'yan Najeriya da su ƙaɗa wa Atiku ƙuri'arsu a zaɓe mai zuwa.

Karin bayani daga Okonkwo

Sahara Reporters ta rahoto Okonkwo yana cewa Gwamna Hope Uzodimma ya bayar da shawarar cewa Tinubu zai tsaya a ofis domin mai da hankali kan gwamnati yayin da su kuma za su ci gaba da yaƙin neman zaɓe.

"A zahiri jam'iyyar APC tana shaida wa Shugaban Ƙasa ne ta kaikaice da ya zauna a asibiti ya kula da lafiyarsa maimakon ya riƙa fitowa yana ba su kunya ta hanyar faɗuwa babu gaira babu dalili da kuma yin maganganun da ba su fita sarai a taruka.
"Tinubu ya tabbatar da cewa ba zai tarayya a yaƙin neman zaɓe ba amma zai riƙa magana da 'yan Najeriya daga ofis dinsa. Na yarda cewa ya kamata Shugaban Ƙasa ya sauka daga matsayinsa saboda ba shi da lafiya domin Najeriya ta samu shugaba mai ƙoshin lafiya da ya dace.
Kenneth Okonkwo da Atiku Abubakar
Kenneth Okonkwo yana gaisawa da dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Shekarau ya yabi Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa gabanin zaɓen 2027, manyan shugabannin siyasa daga Arewa sun yi taro a Abuja domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Magana ta fito daga bakin minista, an ji adadin shekarun da Tinubu ke buƙata a kan mulki

Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau da tsohon Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, ta gana da Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Dr. Nentawe Yilwatda.

Yayin gabatar da tsarin aikinsu, Sanata Shekarau ya bayyana cewa an kafa A4A ne domin cika giɓin tsarin APC na ƙasa ta hanyar yin amfani da gogaggun masu dabarun siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng