An saki 'yan kasuwar kantin kwari 18 da a ka sace
- Kungiyar 'yan kasuwan Arewa sun tabbatar da sakin 'yan kasuwan da a ka sace
- Kungiyar ta bayyana haka ne a wata hira ta wayar tarho ta bakin wani jigon kungiyar
- Shugaban kungiyar ya tabbatar da cewa sai da a ka biya kudin fansa kafin sakin 'yan kasuwan
'Yan kasuwar Kantim Kwari goma sha takwas da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Aba a jihar Abia sun an sake su dakyar.
Ku tuna cewa an sace yan kasuwar ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Janairu, a Okene, jihar Kogi, akan hanyarsu ta zuwa Aba don siyan kayan masaku
Shugaban kungiyar 'yan kasuwar Arewa na Najeriya, Alhaji Abubakar Babawo ya tabbatar da sakin 'yan kasuwar a wata hira ta wayar tarho da jaridar The PUNCH a Kano ranar Lahadi.
KU KARANTA: Wani dan Najeriya ya kirkiri hanyar samawa matasa aiki a Amurka
Ya ce 'yan kasuwar da a ka sace an sake su ne da yammacin ranar Asabar.
“Yan kasuwar kano 18 da ke cikin yan kasuwar 27 sun kubuta a yammacin Asabar. Sun kwana a kaduna kuma yanzu haka suna kan hanyar zuwa kano.
"Muna tsammanin su yau a Kano kamar yadda muke tattaunawa da su.
“Mun tattauna da wasu daga cikinsu. Dukkansu an sake su. Suna nan lafiya kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Kano.” inji shi.
Babawo ya tabbatar da cewa an biya kudin fansa amma ya ki bayyana adadin kudin da aka biya don sakin su.
KU KARANTA: 2013: Rikici kan neman kujerar gwamnan Kaduna
"Ba zan iya fada muku adadin kudin da aka biya ba don a sako su amma an biya fansa kafin a sake su," in ji shi.
A wani labarin daban, Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), na karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, Alhaji Sani Gyare, ya ce bashi da kudin fansa N50m da masu satar mutane ke nema domin sakin yaran sa guda bakwai.
An sace yaran Gyare su bakwai a ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da ‘yan bindiga suka afka gidan su da ke Maru. Yaran su ne Bashar, Abubakar, Haruna, Habibah, Sufyan, Armaya’u da Mubarak.
Da yake magana da jaridar Sunday Tribune a ranar Asabar, jigon jam'iyyar ya bayyana cewa yana adawa da biyan kudin fansa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng