2013: Rikici kan neman kujerar gwamnan Kaduna
- Rikici ya barke tsakanin sanatan Kaduna ta tsakiya da kakakin majalisar jihar ta Kaduna
- Sanatan hasashe na nuna yana harin kujerar gwamnatin jihar a zabe mai gabatowa 2023
- Shi kuwa kakakin majalisar, ya kasancewa mai harin kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya
Kwanan nan, rashin fahimta da fito na fito tsakanin sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Uba Sani da kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Zailani, ya qara qamari. Manyan 'yan siyasan biyu sun fito ne daga yankin Kaduna ta tsakiya.
Masana sun bayyana 'yan siyasar biyu da cewa suna gwagwarmaya ce ta neman daukaka da iko a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a shiyyar.
Yankin sanata na tsakiya, wanda Uba Sani ke wakilta, ya hada da kananan hukumomin Birnin Gwari, Chikun, Giwa, Igabi, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu da kuma Kajuru. Zailani daga wannan yanki yake kuma yana wakiltar mazabar jihar Igabi.
Kakakin majalisar dokokin a baya-bayan nan ya zargi Sanata Uba Sani da rashin tabuka wani abin a-zo-a-gani a yankin mazabarsa ta Igabi.
Sani, wanda tsohon babban mataimaki ne na musamman ga shugaban kasa Olusegun Obasanjo, an ce yana sa ido ne a kujerar mulkin Kaduna a zaben 2023 mai zuwa.
Zailani, wanda ya zama kakakin majalisar jihar a ranar 25 ga Fabrairu, 2020, masu lura suna cewa shi ma yana harin kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a zaben 2023 mai zuwa.
KU KARANTA: Babu cutarwar da za ta sami Bishop Kukah - CAN
Sai dai masu sukar Sani, sun ce ba za a amince da shi ba, saboda ya ci amanar abokinsa na kusa, Shehu Sani don burin kansa na siyasa.
Suna ganin shi a matsayin wanda ba shi da cikakken matsayi a siyasance, kasancewarsa wanda ya ci gaba da dogaro da Gwamna El-Rufai don share fagen harkar siyasarsa.
Tuni, jita-jita ta fara daga wadanda ke kusa da sansanin Uba Sani cewa idan gwamnan ya gaza amincewa da burinsa na gwamna, zai iya daukar damar sa a cikin sansanin tsohon Gwamna Ahmed Markarfi don komawa jam'iyyar PDP.
“Kun san yadda ‘yan siyasar Nijeriya ke aiki; idan suna jin ba za su iya cimma burinsu na siyasa a cikin jam’iyyarsu ba, sai su nemi hanyar sauya sheka.
"Idan har APC ta hana shi tikiti, Sani zai bukaci tabbaci daga PDP da Makarfi kafin ya yi irin wannan kasada, amma mutane daga sansaninsa suna ta kai kawo, ”in ji wata majiya da ke kusa da sansanin.
Kakakin majalisa Zailani, a daya bangaren, ya kasance mai kaifin kishin talakawa tsawon shekaru kuma ya kasance dan majalisa a karo na hudu.
Zailani, wanda a yanzu shi ne shugaba, kungiyar masu magana da yawun Arewa, an ce yana da tunanin kansa, kuma masu lura da al'amuran siyasa na cewa yanayin halayyarsa ta sa ya kasance mai cin gashin kansa.
Kodayake dimbin matasa daga mazabarsa suna kaunarsa, amma masu adawa da Zailani suna yi masa kallon tuhuma, inda wasu ke cewa, "har ma gwamnan ba zai iya hango shi da sauri ba."
KU KARANTA: Da duminsa: An fara yi wa mutane jabun rigakafin Korona
Wasu majiyoyi daga cikin APC a jihar sun shaida wa Aminiya a ranar Lahadi cewa yayin da Gwamna El-Rufai ya dukufa kan mayar da hankali kan shugabanci da kuma share hanyar da zai cimma burinsa na nan gaba, ga alama akwai rikici a cikin gidan siyasarsa.
Wasu kuma na ikirarin El-Rufai da kansa na iya kasancewa a bayan yunkurin Zailani na kawar da burin Sani kamar yadda suke ikirarin cewa gwamnan ya nuna shakku kan sanatan na iya shugabantan jihar.
A wani labarin daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya amince da fitar da Naira miliyan 100 don sayo Sarrafaffen Abinci mai Gina Jiki (RUTF) da ake bukata don kula da yara masu fama da tamowa.
Salisu Lawal, Daraktan, Hukumar Kula da Taimakon Bunkasa, Tsare-tsare da Kasafin Kudi, ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Kaduna ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa ma'aikatar kudi ta jihar ta saki adadin da aka amince da shi a ranar 31 ga Disamba, 2020.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng