Zaɓen 2027: Abin da Tinubu Ya Faɗa wa Taron Ƴan Tsintsiya kan Shirin Kamfen
- Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da kwamitin kamfen APC na 2027, inda ya bukaci mambobinsa su hada kai
- Kashim Shettima ya soki Atiku Abubakar da Peter Obi kan kalamansu, yayin da Nentawe Yilwatda ya bayyana shirin kwamitin
- Hope Uzodimma da wasu manyan ‘yan siyasa sun nuna goyon bayan sake zaben Tinubu, tare da yabawa manufofin gwamnatin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa karkashin jam’iyyar APC domin tunkarar zaben 2027.
A yayin bikin da aka gudanar a Cibiyar Taro ta Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, ya bukaci shugabannin jam’iyyar da mambobin kwamitin su hada kai, su jajirce wajen ganin ya samu damar zarcewa kan kujerarsa.

Source: Facebook
Abin da Tinubu ke bukata daga kwamitin
Tinubu ya bayyana cewa nasarar da APC ta samu a zaben baya ba ta isa ba, domin dole ne jam’iyyar ta sake yin nasara a 2027, kamar yadda Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook.
Ya bukaci masu ruwa da tsaki su tabbatar da samun goyon bayan masu zabe a mazabu, kananan hukumomi da jihohi. Ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta da kuma aiwatar da manufofin ajandar Renewed Hope, yayin da kwamitin ke neman goyon bayan jama’a.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yaba wa Tinubu bisa kokarinsa na karfafa dimokuradiyya. Sai dai ya soki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kan kalaman da ya ce suna rage darajar mukamin shugaban kasa.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa kwamitin zai gudanar da yakin neman zabe a matakai daban-daban, tun daga mazabu har zuwa jihohi.
Ya ce za su mayar da hankali wajen sanar da ‘yan Najeriya ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar da kuma manufofin da take son cimmawa, domin samun karin goyon baya a zaben mai zuwa.

Source: Facebook
Gwamna ya kwarara yabo ga gwamnatin Tinubu
A nasa jawabin, gwamnan Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma, ya ce manufofin gwamnatin Tinubu za su taimaka wajen saukaka yakin neman zaben.
Ya yaba wa shugaban kan dakatar da tallafin man fetur da sauye-sauyen da aka yi a tsarin musayar kudaden waje da haraji.
Uzodimma ya yi ikirarin cewa tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 4.43 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 4.23 cikin 100 na shekarar da ta gabata, duk da kalubalen da wasu daga cikin matakan suka jawo wa jama’a.
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, gwamnan Anambra, Charles Soludo, da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu domin ya sake lashe zaben shugaban kasa a 2027.
Wike, wanda mamba ne a jam’iyyar PDP, ya ce yana goyon bayan Tinubu ne saboda yadda yake fuskantar matsalolin da gwamnatocin baya suka kasa magancewa.
Tinubu ya yi subutar baki a taro
An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi subutar baki, ya kira kansa gwamna maimakon shugaban ƙasa yayin jawabi a wajen ƙaddamar da kamfen APC.

Kara karanta wannan
Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan ƙoƙarin neman sake zaɓensa a wa’adi na biyu na shekaru huɗu.
Kwamitin kamfen ya ƙunshi manyan ’yan APC da kuma wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da Nyesom Wike da Ademola Adeleke.
Asali: Legit.ng

