‘Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi 4, sun kwato shanu 200 da makamai a Zamfara

‘Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi 4, sun kwato shanu 200 da makamai a Zamfara

- Rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara sun samu nasarar cafke wasu da ake zargi da satar shanu sama da 200

- Rundunar ta kwato shanun da bindigogi hade da alburusai a hannun mutanen da a kamen

- Hakazalika rundunar ta bukaci masu ruwa da tsaki a jihar da su kara bada hadin wajen kawar bata gari a yankin

Rundunar ‘yan sanda a Zamfara ta cafke mutum hudu da ake zargi da kisan wani Bafulatani makiyayi, Vanguard News ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a Gusau a ranar Lahadi, Kwamishinan 'yan sanda, Abutu Yaro, ya ce rundunar ta kuma kwato shanu 200 da suka salwanta sakamakon jajircewa wajen yaki da aikata laifuka.

Ya kara da cewa an kwato wasu makamai, kuma rundunar ta samu nasarar sakin akalla mutane takwas da aka sace makonni uku da suka gabata.

KU KARANTA: Wani dan Najeriya ya kirkiri hanyar samawa matasa aiki a Amurka

‘Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi 4, sun kwato shanu 200 da makamai a Zamfara
‘Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi 4, sun kwato shanu 200 da makamai a Zamfara Hoto: Vanguard News
Source: UGC

"Mun kwato akalla shanu 200 da aka sace, da bindigogin AK 47 guda biyar, da motoci uku da kuma alburusai masu yawa," in ji shi.

A cewar kwamishinan, sulhun da gwamnatin jihar ke jagoranta ya samar da sakamako mai yawa, ciki har da mika bindigogi AK-47 guda uku da kuma durin harsasai 47.

"Sakamakon ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya a Karamar Hukumar Shinkafi, mun kwato bindiga kirar AK-47 guda daya tare da mujallu biyu da harsasai masu rai 18," in ji shi.

Yaro ya sake bayyana cewa, rundunar a shirye take da ta kasance tare da masu ruwa da tsaki a cikin jihar don tabbatar da yaki da aikata laifuka da tashe-tashen hankula.

KU KARANTA: 2013: Rikici kan neman kujerar gwamnan Kaduna

"Za mu ci gaba da aiwatar da zaman lafiya, za mu ci gaba da yin ma'amala mai ma'ana tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin kawar da jihar daga dukkan nau'ikan 'yan ta'adda masu dauke da makamai," in ji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel