Reshe na Neman Juyewa da Mujiya, EFCC Ta Fara Binciken Atiku ana Daf da Zaɓe
- Hukumar EFCC ta karɓi sabon ƙorafi da ke neman gurfanar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar
- Tsohon ɗan majalisar wakilai, Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, ya nemi a sake duba binciken 2006 da rahoton majalisar Amurka na 2010
- Agbonayinma ya zargi EFCC da gazawar ɗaukar mataki, yana mai cewa ya kamata doka ta yi aiki daidai ga kowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta karɓi sabon ƙorafi da ke neman a gurfanar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan zargin aikata laifukan kuɗi.
An shigar da ƙorafin ne a hannun hukumar ta hannun tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, wanda ya buƙaci a sake duba binciken da aka gudanar a baya kan zarge-zargen.

Source: Twitter
Bukatar da aka tura wa EFCC
Agbonayinma ya kuma buƙaci hukumar ta yi la'akari da wani rahoto da ƙaramin kwamitin majalisar dattawan Amurka ya fitar daga baya, cewar Leadership.
Agbonayinma ya ce EFCC ta amince da karɓar ƙorafinsa mai kwanan wata 27 ga Agusta, 2026, wanda hukumar ta karɓa ranar 1 ga Satumba.
An miƙa ƙorafin ne ta hannun lauyansa, Cif Hannibal Egbe Uwaifo, SAN, inda aka buƙaci hukumar ta sake duba sakamakon binciken da ta gudanar a baya tare da ɗaukar matakin da ya dace.
Tsohon ɗan majalisar ya je hedikwatar hukumar EFCC da ke Jabi, Abuja, inda ya tabbatar da ƙorafin a hukumance tare da amsa tambayoyin masu bincike.
Da yake magana kan lamarin, Agbonayinma ya dage cewa bai kamata a bar batun ba tare da warwarewa ba, yana mai jaddada cewa doka ta shafi dukkan 'yan Najeriya, ba tare da la'akari da matsayinsu na zamantakewa ko siyasa ba.
Ya ce:
“Ina so in gode wa 'yan Najeriya, EFCC da waɗanda ke yi mini addu'a a wannan fafutuka. An tanadi dokoki ne domin masu kuɗi da talakawa. Bayan EFCC ta yi aiki mai kyau, bai kamata a ɓoye sakamakon aikinta ba.”
A cikin ƙorafin, Agbonayinma ya buƙaci hukumar ta sake duba rahotonta na watan Satumba na 2006 kan Atiku da kuma rahoton ƙaramin kwamitin dindindin na binciken harkokin gudanarwar gwamnati na majalisar dattawan Amurka, wanda aka fitar ranar 4 ga Fabrairu, 2010.
Ya yi iƙirarin cewa waɗannan takardu biyu za su iya zama hujjar sake binciken zarge-zargen da kuma ɗaukar ƙarin matakai daga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawar.
Agbonayinma ya bayyana rashin ɗaukar mataki kan lamarin a matsayin gazawar hukumar wajen sauke nauyin da ke kanta.
Sannan ya ce sake duba batun zai nuna cewa hukumar ta himmatu wajen tabbatar da cewa ana hukunta masu tasiri a siyasa bisa tanadin doka.
Ya kuma bayyana cewa ya shigar da ƙorafi ga shugaban Amurka, Donald Trump, kan zarge-zargen.
A halin da ake ciki, kakakin EFCC, Dele Oyewale, bai mayar da martani ga saƙonnin neman ƙarin bayani kan matsayin binciken ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
APC ta fadi dalilin faduwar Tinubu a Kaduna
Kun ji cewa mai magana da yawun APC a Kaduna, Mohammed Sani Haruna, ya yi magana kan rashin nasara da Bola Tinubu ya yi a zaben 2023 a jihar.
Haruna ya ce salon mulkin Gwamna Uba Sani ya sauya siyasar Kaduna, inda ya haɗa mutane daga addinai, ƙabilu da jam'iyyun siyasa daban-daban.
APC ta ce tana fatan samun ƙuri'u miliyan biyu a Kaduna domin sake zaɓen Tinubu a 2027, tare da shirya babban gangamin kamfen.
Asali: Legit.ng


