Ma'aikatar albarkatun man fetur ta kashe N98.4m a buga takardun wayar da kai

Ma'aikatar albarkatun man fetur ta kashe N98.4m a buga takardun wayar da kai

- Majalisar dattijai ta zargi ma'aikatar albarkatun man fetur da kashe kudi ba kan ka'ida ba

- Majalisar ta bayyana cewa ba a bi ka'idar gwamnati wajen kashe N98.4m don buga takardun wayar da kan jama'a ba

- Sai dai ma'aikatar ta yi martanin yadda ta kashe tare da musanta rashin bin ka'ida da a ka zarge ta dashi

Kwamitin majalisar dattijan da ke kula da asusun gwamnati ta tuhumi ma’aikatar albarkatun man fetur da kashe N98.4m don buga takardun wayar da kan jama’a game da Dokar Masana’antar Man Fetur ba tare da bin ka’ida ba.

Kwamitin, wanda Sanata Matthew Urhoghide ya jagoranta, ya ci gaba da tambayar bayan la’akari da rahoton shekarar 2015 na Babban Odita-Janar na Tarayyar, Aminiya ta ruwaito.

Tuhumar ta ce: “Sabanin tsarin siye da siyarwa, shigar da kudi N98.4m an yi su ne don goyon bayan wani kamfani don buga takardun shirin wayar da kai game da Dokar Masana’antar Man Fetur.

KU KARANTA: ‘Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi 4, sun kwato shanu 200 da makamai a Zamfara

Ma'aikatar albarkatun man fetur ta kashe N98.4m a buga takardun wayar da kai
Ma'aikatar albarkatun man fetur ta kashe N98.4m a buga takardun wayar da kai Hoto: Pointblank News
Source: UGC

Kwamitin ya zargi hukumar ma'aikatar da rashin bin ka'idar gwamnati wajen ba da kwangilar. Kwamitin ya kuma bukaci sakataren dindindin na ma'aikatar da ya dauki matakan ladabtarwa a kan jami'an da suka tafka kuskuren.

Ma'aikatar, a cikin rubutaccen amsar da ta bayar, ta ce: “An yi cikakken sanarwa. An zaɓi M / s Dangrace & Partners Ltd bisa ga tabbatar da ƙwarewarsu.

“Ya kamata a bayyana cewa an gabatar da takardar nuna sha'awa kafin a ba da izinin bayar da aiki da kuma samar da takardun na PIB.

"Sashen ya bi ka'idojin da suka dace." A wata tambayar kuma, rahoton binciken ya ce sabanin tsarin biyan kudi ta Gwamnatin Tarayya, an biya N39.7m ga ma’aikata 178 na ma’aikatar domin sanya ido kan aikin a shekarar 2014.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun kame wanda ya kawo kudin fansar 'yan uwansa

A wani labarin daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman manyan mutane da su yi adalci wajen sukar gwamnatinsa ta hanyar duba halin da kasar ke ciki kafin hawan gwamnatin yanzu, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a fadar gwamnati da ke Abuja, yayin da ya karbi bakuncin Reverend Yakubu Pam, Sakatare Janar na Hukumar Alhazai ta Kiristocin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel