Gobara ta lashe shaguna 62 a Legas
- Gobara a wata kasuwa dake cikin jihar Legas ta cinye shaguna 62
- Wani gida mai dauke da dakuna 24 shi ma ya kone kurmus a kusa da kasuwar
- Hukumar kashe gobara sun samu nasarar kashe wuta ba tare da rasa rai ko rauni ba
Akalla shaguna 14 ne suka lalace gaba daya a gobara a Kasuwar Ijesa da ke Surulere Legas.
Gobarar da ta tashi a daren Asabar ta kuma kone shaguna 48 tare da lalata gidan da ke kusa mai dakuna 24, Aminiya ta ruwaito.
Lamarin gobarar da ya fara da misalin karfe 5 na yamma a ranar Asabar ya kwashe sama da awanni hudu, tare da 'yan kasuwa 62 da kuma kimanin gidaje 28 da lamarin ya shafa.
Kodayake ba a rasa rai ba kuma ba a samu rauni ba, amma hukumomin bayar da agajin gaggawa sun tabbatar da cewa gobarar ta tashi ne daga wani daki da aka sauya zuwa shago.
KU KARANTA: Jihar Ekiti zata kashe N1.4bn Domin karfafa 'yan bangan Amotekun
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), da Hukumar kashe gobara ta Tarayya da ta jihar sun sami nasarar kashe wutar baki daya.
Ko’odinetan NEMA na Ofishin Yankin Legas, Ibrahim Farinloye, ya ce wutar ta fara ne ta hanyar silinda da ake amfani da shi wajen dafa abinci.
KU KARANTA: Amotekun sun kashe uba da 'ya'yansa biyu a Oyo
Ya ce masu kawo dauki sun fuskanci kalubale na rashin samar da ruwa kuma motocin kashe gobara biyar daga tarayya, jihar da LRU sai da suka tafi da tazara daga wurin domin samun ruwa.
A wani labarin, Wani sananne a kafofin sada zumunta, Ipadeola Oriyomi, ya zargi ‘yan sanda da kin sanya shi a wani kebantaccen waje bayan da an tabbatar yana dauke da cutar COVID-19, The Punch ta ruwaito.
Oriyomi wanda ya koka a shafukan sada zumunta ya ce, ‘yan sandan ofishin Maroko da ke Legas ne suka kama shi a wani gidan rawa da dare a tsibirin Victoria.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng