Wasu masu bincike a UNILORIN sun ba da shawarar amfani da abarba don magance COVID-19

Wasu masu bincike a UNILORIN sun ba da shawarar amfani da abarba don magance COVID-19

- Wasu masu bincike sun gano cewa abarba kan iya yaki da kwayar cutar Korona

- Masu binciken sun gudanar da bincike mai zurfi kan abubuwan da abarba ke dauke dashi

- Sun yi kira ga hukumomi masu ta cewa a fannin da su duba al'amarin don kulawa da Korona

Wata tawagar masu bincike a Jami'ar Ilorin (UNILORIN) sun gano karfin Bromelain wanda aka samo daga 'ya'yan itacen abarba don rage karfin kwayar cutar COVID-19, Vanguard ta ruwaito.

A cewar Jami'ar Ilorin a wata sanarwa da aka bayar a ranar Litinin, binciken ya kasance tare da Farfesa Bamidele Owoeye, Shugaban, Sashin Ilimin Kimiyyar Jiki, da Mista Ahmed Bakare, dalibin PhD a jami'ar.

An buga littafin mai taken: “Bromelain reduced Pro-Inflammatory Mediators as A Common Pathway that Mediate Antinociceptive and Anti-anxiety Effects in Sciatic Nerve Litigated Wistar Rats.”

KU KARANTA: Gobara ta lashe shaguna 62 a Legas

Wasu masu bincike a UNILORIN sun ba da shawarar amfani da abarba don magance COVID-19
Wasu masu bincike a UNILORIN sun ba da shawarar amfani da abarba don magance COVID-19 Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Binciken, wanda aka gudanar a jami’ar kuma ya samo asali ne daga karatun digirin digirgir na Bakare, ya nuna cewa ‘ya’yan itacen abarba za su iya zama masu amfani ga jiki, musamman wajen maganin ciwon da ke faruwa sakamakon raunin jijiyoyin da ake kira Neuropathic.

"Ya kuma bayyana cewa yayin da bromelain, wanda aka samo daga 'ya'yan itacen abarba, zai iya taimakawa jin zafi daga raunin jijiyoyin, shi ma yana ciyar da jijiyoyin da suka ji rauni ta haka yana taimakawa rage raunin," in ji shi.

Owoeye ya kara da cewa bromelain na da karfin da zai bunkasa aiyukan jijiyoyin da suka ji rauni ta hanyar rage aiyuka da maida hankali kan sinadarai masu zogi wadanda ake samarwa yayin da jijiyoyin suka ji rauni.

Don haka, ya ja hankalin hukumomin da abin ya shafa kan muhimmacin bromelain / abarba a magance COVID-19 saboda ababen abarba suna dauke da bromelain wanda ke rage karfin cytokines, wanda ke cikin abubuwan da ke lalata COVID-19.

KU KARANTA: Tsohon shugaban kwastam da wani sun mayar da N8bn asusun gwamnati

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) a ranar Juma’a ta bayyana cewa ba ta amince da duk wani rigakafin COVID-19 ba, The Nation ta ruwaito.

Ta yi gargadin alluran rigakafin bogi sun fara yawo a cikin kasar, inda ta yi kira ga jama'a da kar su sayi irin wadannan magunguna domin suna iya haifar da cututtuka irin na COVID-19 kuma za su iya haifar da mutuwa.

Ta kuma bukaci cibiyoyin gwamnati, hukumomi da manyan kamfanoni da kada su yi odar allurar rigakafin ta COVID ba tare da tabbatarwa daga NAFDAC ba idan an amince da maganin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.