Wasu daga cikin 'yan ta'addan Boko Haram Kiristoci ne - Gwamna Zulum

Wasu daga cikin 'yan ta'addan Boko Haram Kiristoci ne - Gwamna Zulum

- Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana cewa ba musulmai kadai bane 'yan Boko Haram

- Gwamnan ya bukaci 'yan kudu da arewa kowa ya dauka Boko Haram da Najeriya suke yaki

- Gwamnan yayi kira ga a kiyaye kabilanci, raba kan mutane da son kai don ci gaban kasa

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina ganin fitinar da ke faruwa a jihohin arewa maso gabashin jihohin Borno, Yobe da Adamawa a matsayin matsalar arewa; kalubale ne da ya shafi kowa da kowa.

Zulum ya bayyana haka ne a wajen taron karawa juna sani na shekara ta 17 na Gani Fawehinmi wanda Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, reshen Ikeja ta shirya ranar Juma’a.

A cewarsa, mambobin kungiyar ta Boko Haram sun hada da fararen fata, 'yan Asiya, 'yan Afirka, Musulmai da Kirista, Sahara Reporters ta ruwaito.

KU KARANTA: 2013: Rikici kan neman kujerar gwamnan Kaduna

Wasu daga cikin 'yan ta'addan Boko Haram Kiristoci ne - Gwamna Zulum
Wasu daga cikin 'yan ta'addan Boko Haram Kiristoci ne - Gwamna Zulum Hoto: Daily Watch Press
Source: UGC

Gwamnan ya danganta fitina da ta'addancin da ake yi a kasar ga yawaitan rashin aikin yi, talauci, da kuma shan muggan kwayoyi, yana mai kira ga 'yan Najeriya da su guji nuna son kai, kabilanci da kuma ra'ayin amfani da addini wajen haifar da rarrabuwa.

Ya kara da cewa ya maye gurbin tsohon Shugaban Ma'aikatansa, wanda dan uwansa Musulmi ne, da Kirista, saboda ya fifita cancanta sama da biyayya. Ya ce wannan ne karo na farko da Kirista zai hau kujerar a jihar.

“Ni dan jihar Barno ne, kuma yawancin ‘ya’yanmu suna cikin Boko Haram. Ba na musun gaskiyar. Amma kuma, mutane da yawa suna ɗaukar nauyin su a duk faɗin duniya. Daga cikin Boko Haram, muna da fararen fata, 'yan Asiya, 'yan Afirka, Musulmi da Kirista,” in ji Zulum.

“Dole ne mu daina ganin wannan fitinar a matsayin matsalar Arewa.

"Tazarar da ke tsakanin jihar ta Borno da ta jihar Legas ta kai kimanin kilomita 1,700, amma fa ku kula idan jihar ta Borno ba ta da zaman lafiya, sauran bangarorin kasar nan ba za su taba zama cikin lumana ba.

KU KARANTA: Bani da N50m kudin fansa - mahaifn 'ya'ya 7 da a ka sace

"Dole ne mu hada kai mu yaki wadannan mahara. Mun ga abin da ya faru a Libya, Iraki da sauran ƙasashe. Gina zaman lafiya da haɗin kan jama'a suna da matukar mahimmanci wajen ƙarfafa ƙarfin al'ummominmu.

“Har sai mun kawar da son zuciya, kabilanci da kuma amfani da addini, kafin mu samu daidai a kasar nan.

"Tsarin mulki ya bayyana karara kan bukatar zaman lafiya a tsakaninmu baki daya, shi yasa ma aka sanya tsarin dabi'ar tarayya a cikin kundin tsarin mulki, amma an ci zarafinsa."

A wani labarin daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Talata ya ba da umarnin daukar likitoci 40 a matsayin kari kan yardarsa da ya yi a baya, domin biyan bukatun kula da lafiya na karuwar al’ummar jihar, Vanguard News ta ruwaito.

Shawarwarin na ranar Talata na zuwa ne watanni hudu bayan da Gwamnan ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 594.

Daga cikin wadanda za a dauka sun hada da: likitoci lafiya 86, ma’aikatan jinya 365 da ungozomomi, masu harhada magunguna 45 da kwararrun masana kiwon lafiya 100 da sauran ma’aikatan tallafi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel