NIN ya zama dole ga jami'an diflomasiyyar kasashen waje -FG

NIN ya zama dole ga jami'an diflomasiyyar kasashen waje -FG

- Gwamnatin tarayya ta bukaci jami’an diflomasiyyar kasashen waje da su yi rajistar NIN

- Gwamnatin tarayya za ta tanadi wajen yin rajistar a ofishin Ma’aikatar Harkokin Wajen ta Tarayya

- Gwamnatin za sanar da ranar 19 ga watan Janairu a matsayin ranar da zasu fara rajistar

Gwamnatin Tarayya ta ce lambar shaidar dan kasa ya zama tilas ga jami’an diflomasiyyar kasashen waje da za su ci gaba da zama a Najeriya na tsawon shekaru biyu ko sama da haka, jaridar Punch ta ruwaito.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dr Isa Pantami, ne ya fadi hakan a cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Fasaha, Dr Femi Adeluyi, ya fitar a ranar Lahadi.

KU KARANTA: 2013: Rikici kan neman kujerar gwamnan Kaduna

BREAKING: NIN ya zama dole ga jami'an diflomasiyyar kasashen waje -FG
BREAKING: NIN ya zama dole ga jami'an diflomasiyyar kasashen waje -FG Hoto: BBC Hausa
Asali: Twitter

Ya ce an kafa cibiyar yin rajista ga jami’an diflomasiyyar kasashen waje a Ma’aikatar Harkokin Wajen ta Tarayya.

Sanarwar ta karanta, “Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dokta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya amince da kafa cibiyar rajistar lambar shaidar dan kasa (NIN) a Ma’aikatar Harkokin Waje ta Tarayya.

“Za a kafa teburin a ranar Talata, 19 ga Janairu, 2021.

KU KARANTA: An saki 'yan kasuwar kantin kwari 18 da a ka sace

“Wannan cibiyar yin rajistar za ta bayar da tallafi ga mambobin diflomasiyyar kuma za a kula da su ta Ma’aikatar Sadarwa ta Tarayya da Tattalin Arziki na Dijital, ta hanyar Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa.

A wani labarin daban, Legit ta ruwaito Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta ce ba za ta katse masu amfani da layin sadarwar ba sakamakon ci gaba da alakanta lambobin shedar kasa (NINs) da katinan SIM.

Daily Trust ta ruwaito cewa NCC a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 6 ga Janairu, ta ce bayanin ya zama dole don kawar da tsoron masu amfani da layuka da sauran jama’a.

An ruwaito mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Adinde yana cewa wani binciken da aka gudanar kwanan nan akwai kusan katinan SIM guda hudu zuwa biyar ga kowane dan Najeriya mai amfani da waya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

https://www.youtube.com/watch?v=i8k-hlQSyAA&feature=emb_title

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.