Ganduje, Shekarau da Sauran Jiga Jigan APC da Suka Shiga Kwamitin Kamfen Abba
- Jam’iyyar APC a Kano ta sanar da kafa kwamitin masu ba da shawara mai mutum 155, domin kula da harkokin kamfen zaɓen 2027
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai jagoranci kwamitin, wanda ya ƙunshi tsofaffin gwamnoni Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje
- Jam’iyyun NDC da ADC ba su sanar da kwamitocin kamfen ba, yayin da NDC ke fama da cire sunan ɗan takararta Aminu Abdulsalam daga jerin INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta sanar da kafa kwamitin masu ba da shawara mai mutum 155, domin zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na 2027.
Kwamitin, wanda zai kasance mafi girman hukuma mai kula da ayyukan kamfen a jihar, zai kasance ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
Manyan jiga-jigan da ke cikin kwamitin sun haɗa da tsofaffin gwamnoni Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje, tare da tsofaffin shugabannin mulkin soja uku na jihar, cewar Premium Times.
An saka tofaffin shugabannin mulkin soja
Tsofaffin shugabannin mulkin sojan sun haɗa da Habibu Shuaibu, Lawan Jafaru-Isa da Yakubu Bako, waɗanda za su taka rawa wajen bayar da shawarwari kan harkokin siyasa.
Shugaban APC na jihar Kano, Umar Doguwa, ya bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da Sanatoci Kawu Sumaila da Rufa’i Hanga.
Haka kuma, kwamitin ya ƙunshi dukkan 'yan takarar APC da mambobin Majalisar Wakilai ta Tarayya da ke wakiltar jihar Kano.
Kwamitin zai samar da jagoranci da tsare-tsare ga babban kwamitin gudanar da kamfen na 2027, wanda za a kafa tare da sanar da sunayen mambobinsa nan gaba.
Sanarwar ta zo ne kwanaki uku kacal bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu mutane 16 sun bayyana cikin jerin sunayen ƙarshe na 'yan takarar gwamna a jihar.
INEC ta cire sunan Gwarzo cikin yan takara
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ce ta fitar da jerin sunayen a ranar Asabar 10 ga watan Oktobar 2026.
A halin da ake ciki, jam’iyyun adawa, ciki har da Nigeria Democratic Congress (NDC) da African Democratic Congress (ADC), ba su sanar da kwamitocin kamfen ɗinsu ba.
A yanzu haka, NDC na ƙoƙarin shawo kan matsalar cire sunan ɗan takararta na gwamna, Aminu Abdulsalam, daga jerin sunayen da INEC ta fitar, cewar Punch.
Cire sunansa ya girgiza fagen siyasar jihar, inda jam’iyyar ke neman hanyoyin shari’a da na gudanarwa domin ceto damar da take da ita a zaɓen gwamnan.
INEC ta magantu kan cire sunan Pantami, Gwarzo
A wani labarin, an ji cewa Hukumar INEC ta yi bayanin dalilin cire sunayen wasu yan takarar gwamna daga jam'iyyu daban-daban.
Hukumar INEC ta bayyana dalilin da ya sa ba a saka sunayen Isa Ali Pantami da an takarar gwamnan Kano a NDC, Abdulsalam Aminu Gwarzo.
INEC ta bai wa jam’iyyun siyasa wa’adin ranar 24 ga Oktoba domin sanar da ita korafe-korafen cire sunayen ‘yan takararsu saboda daukar matakin da ya dace.
Asali: Legit.ng

