Ana zargin Wani Bawan Allah da Kashe Matarsa A Kasar Italia

Ana zargin Wani Bawan Allah da Kashe Matarsa A Kasar Italia

- Wani mutum mazaunin kasar Italiya asalin dan Najeriya ya kashe matarsa har lahira

- Mutumin an bayyana ya kan samu sabani tsakaninsa da matar kafin daga bisani ya kasheta

- An bayyana cewa ya jima yana cewa zai kashe ta kuma babu abinda zai faru

An kama wani dan Najeriya, Moses Osagie bayan ya kashe matar sa, Temitope, a Italiya.

Da yake magana da SaharaReporters, dan uwan marigayiyar, Sunday Obalakun, ya ce Osagie ya buge Temitope ya kashe ta a ranar Lahadi.

Sunday, wanda ya tabbatar da kame wanda ake zargin da ‘yan sanda na Italiya suka yi, ya ce ya yi magana da 'yar uwarsa minti 20 kafin lamarin ya faru.

KU KARANTA: Gobara ta lashe shaguna 62 a Legas

Ana zargin Wani Bawan Allah da Kashe Matarsa A Kasar Italia
Ana zargin Wani Bawan Allah da Kashe Matarsa A Kasar Italia Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

Ya ce, “Duk da cewa sun kasance suna samun sabani kafin lamarin, mijin ya sha fada sau da yawa cewa zai kashe ta kuma ba abin da zai faru, kuma abin da ya yi kenan a ranar Lahadi.

“Muna kira ga gwamnatin Italiya da ta dauki matakan da suka dace don kada ‘yar uwata ta mutu a banza; ta kasance mabuɗin dangi.

“Haka kuma, ina son su saki gawar‘ yar uwata ga gwamnatin Najeriya domin a binne ta kamar yadda al’adarmu ta tanada.

“Ta kasance matar gida; tana kusa da duk yan uwanta kuma tana matukar kulawa. Ta kasance mai kirki kamar kowace mace 'yar Najeriya. Tana da yara uku tare da shi.”

An sha samun irin wadannan kararrakin da suka shafi ‘yan Nijeriya a kasashen waje.

KU KARANTA: Tsohon shugaban kwastam da wani sun mayar da N8bn asusun gwamnati

Misali, a ranar 18 ga Disamba, 2020, Benjamin Okigbo, wani likita dan Najeriya mazaunin Amurka, ya shake wuyan Theresa Okigbo, matarsa, har lahira kafin ya kashe kansa a gidansu da ke Greatwood, Texas.

A wani labarin daban, Wata yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @ayeesh_chuchu ta bayyana cewa soyayya da namiji mai mata yana da tarin takura da tauye romon jin dadin soyayyar.

@ayeesh_chuchu ta bayyana cewa irin wannan soyayya tamkar gayar tuwo babu miya ne saboda mutum ba zai samu cikakken lokacin kasancewa tare da masoyin nasa ba sai dai idan ya yi nisa da iyalinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.