Abubuwan Boye Sun Fito Fili, Jakadar Amurka Ta Rasa Aikinta a Gwamnatin Trump

Abubuwan Boye Sun Fito Fili, Jakadar Amurka Ta Rasa Aikinta a Gwamnatin Trump

  • Fadar White House ta buƙaci jakadar Amurka a Girka, Kimberly Guilfoyle, ta yi murabus bayan zarge-zargen sun fara yawaita a kanta
  • Rahotanni sun yi zargin cewa ana zargin jakadar ta bayar da damar ganawa da jami'an gwamnatin Donald Trump a madadin kuɗi da kyaututtuka
  • Guilfoyle ta musanta zargin, tana mai cewa za ta kare sunanta, martabarta da mutuncinta a kowane irin mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump ya sallami jakadar Amurka a Girka, Kimberly Guilfoyle, daga aiki, inda ya bukaci ta yi murabus ba tare da bata lokaci ba.

Hakan ya biyo bayan wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai da suka yi zargin cewa ta bayar da damar samun ganawa da jami'an gwamnatin Shugaba Donald Trump saboda an bata cin hancin kuɗi, kyaututtuka da wasu alfarma.

Kara karanta wannan

Wai Trump ya nemi afuwar Tinubu kan wasu zarge zarge? Ga abin da aka binciko

Kimberly Guilfoyle
Jakadar Amurka a kasar Girka mai barin gado, Kimberly Guilfoyle Hoto: Nicolas Koutsokostas/NurPhoto
Source: Getty Images

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Litinin cewa yana duba yiwuwar korar Guilfoyle, wadda a baya ta yi shirin aure da ɗansa, Donald Trump Jr, kamar yadda BBC News ta ruwaito.

Da yake magana da manema labarai a ranar Talata, Shugaba Trump ya ce:

“Tana yin aiki mai kyau, amma ba mu ji daɗin abin da muke karantawa ba.”

An umarci jakadar Amurka ta yi murabus

Sakatariyar yaɗa labarai ta White House, Katie Zacharia, ta tabbatar da cewa an buƙaci Guilfoyle ta yi murabus, inda ta bayyana ta a matsayin mai muhimmanci ga gwamnatin Trump.

“Ta kasance wata babbar gata ga tawagarmu, kuma muna yi mata fatan alheri,” in ji Zacharia yayin wani taron manema labarai.

Dalilin rasa aikin Kimberly Guilfoyle

Matakin ya biyo bayan jerin rahotannin da suka fara fitowa a watan da ya gabata, waɗanda suka tayar da tambayoyi kan halayen Guilfoyle a matsayinta na jakadiya tare da zargin cewa ta yi amfani da muƙaminta wajen fifita wasu buƙatu na kashin kanta.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, rundunar yan sanda ta bayyana dalilin kama tsohon gwamna a Najeriya

Wasu 'yan majalisar dokokin Amurka sun nuna damuwa kan rahotannin, waɗanda suka haɗa da zargin cewa Guilfoyle ta yi barazanar amfani da tasirin Amurka wajen raunana gwamnatin Girka.

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi ga menama labarai kan yakin Iran Hoto: Aaron Schwartz
Source: Getty Images

i dai Guilfoyle ta musanta aikata wani laifi, tana mai jaddada cewa biyayyarta ga Trump da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ba ta sauya ba.

Ta ƙara da cewa:

"Waɗannan zarge-zargen ƙarya ne, kuma na yi niyyar kare sunana, martabata da mutuncina da dukkan ƙarfina.”

Wani ɗan kasuwa Ba’amurke mai suna Eric Deters ya ya shaida wa cewa Guilfoyle ta karbi kudin goro ta bayar da damar ganawa da jami'an gwamnatin Trump.

A cewar rahoton, a wani lokaci ta nemi ya biya mata bashin katin cire kuɗi na Dala 100,000, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Amurka ta kakabawa ICC takunkumi

Kun ji cewa Amurka ta kakaba takunkumi kan kotun ICC, lamarin da ya sa ƙasashe da dama ciki har da ƙawayen Amurka suka soki matakin na Shugaba Donald Trump.

Hadimin Trump, Marco Rubio ya sanar da cewa Washington za ta dakatar da mu'amala da kotun, yayin da Shugaba Donald Trump ya ce ba zai taɓa yarda kotun ta hukunta 'yan Amurka ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262