Wike Ya Jikawa Gwamnonin APC Aiki kan 2027 bayan an Taru a wajen Tinubu
- Nyesom Wike ya bukaci gwamnonin APC su yi kokari wajen tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a jihohinsu a zaben 2027
- Wike ya ce gwamnan da bai kai wa Tinubu nasara a jiharsa ba bai kamata ya yi ikirarin cewa jam’iyyar ta yi nasara ba, ko da Tinubu ya zarce
- A bayanin da ya yi, ministan ya bayyana cewa ya kuduri aniyar tabbatar da nasarar Bola Tinubu a Jihar Rivers da Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bukaci gwamnonin jam’iyyar APC da su dage wajen ganin sun tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jihohinsu a zaben 2027.
Wike ya bayyana hakan ne ranar Laraba a wajen kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a Abuja.

Source: Facebook
Hadimin Wike, Lere Olayinka ya wallafa a Facebook cewa ministan ya ce bai kamata gwamnan da bai lashe jiharsa wa Tinubu ba ya yi ikirarin cewa jam’iyyar ta yi nasara idan shugaban kasar ya sake lashe zabe.
Wike ya gargadi gwamnonin APC
Ministan ya ce nasarar Tinubu a zaben 2027 ba za ta wadatar ba idan wasu gwamnonin jam’iyyar sun kasa tabbatar masa da nasara a jihohinsu.
Ya bayyana cewa ba wai rike mukamai a kwamitin yakin neman zabe ne kadai ke nuna gudummawar mutum ba, illa kokarin da ya yi wajen samar da kuri’un da za su kai ga nasara.
Wike ya ce ya yi farin ciki da ganin an nada shi a matsayin mai kula da yakin neman zaben Tinubu a Jihar Rivers da Babban Birnin Tarayya.
Ya kara da cewa ya shaida wa shugabannin kananan hukumomin Abuja cewa ayyukan raya kasa da ake gudanarwa a yankin za su taimaka wajen jawo wa shugaban kasar kuri’u.

Source: Twitter
Wike zai kawo Rivers da Abuja
Wike ya ce yana da yakinin cewa zai tabbatar da nasarar Tinubu a Jihar Rivers da Abuja, yana mai kalubalantar shugabannin kananan hukumomin babban birnin tarayya da su bayyana ko ba su ganin ayyukan da gwamnatin shugaban kasar ke gudanarwa.
Punch ta wallafa cewa ya ce:
"Idan ba ku kawowa shugaban kasa nasara jiharku ba, kuma ya ci zabe, kada ku ce mun yi nasara. Ba batun cewa ni ne shugaban wannan ko sakataren wancan ko mamba a wani kwamiti ba ne.”
Wike ya kuma bayyana cewa ya taba fadawa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, cewa idan Tinubu bai yi nasara a Legas ba, bai kamata a ce an yi nasara ba.
'Yan adawa na shirin hadaka
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyun adawa shida sun gana da ‘yan takarar shugaban kasa guda biyar a wani yunkuri na karfafa hadin kai gabanin babban zaben 2027.
Jam’iyyun sun hada da ADC, APM, NDC, SDP, PDP da PRP. Tattaunawar ta gudana ne a lokuta daban-daban cikin mako biyu da suka gabata.
A cikin wata sanarwa da Salihu Lukman ya fitar ranar Laraba a madadin jam’iyyun hadin gwiwar, ya bayyana cewa wadanda aka tuntuba sun hada da Atiku Abubakar na ADC, Seyi Makinde na APM, Peter Obi.
Asali: Legit.ng


