Tinubu: Tsohon Shahararren Sanata Ya Jefi Majalisar Tarayya da Zargi Masu Karfi
- Dino Melaye ya zargi Majalisar Tarayya da mika wa Shugaban kasa ikonta, maimakon yin aikin ta na sa ido a Najeriya
- ‘Dan adawan ya soki yadda majalisar ta amince da wasu dokoki cikin gaggawa, tare da nuna damuwa kan yadda ake aiki
- Sanata Dino ya bukaci ’yan majalisa su kare kundin tsarin mulki tare da tabbatar da gaskiya ba bin Bola Tinubu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya zargi shugabannin Majalisar Tarayya ta 10 da barin aikin da yake kansu.
Dino Melaye ya ce an kyale Shugaba Bola Tinubu yana amfani da ikon zartarwa ba tare da isasshen sa ido daga wajen majalisar ba.

Source: Facebook
Sanata Dino Melaye ya caccaki Majalisar tarayya
Jaridar This Day ta ruwaito Dino Melaye, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC, ya soki shugabannin majalisa, yana ganin ba su aikinsu.
Yana ganin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ba su yin abin da ya dace.
Ya ce ba su taka rawar da ta kamata wajen kare kundin tsarin mulki da kuma sanya Gwamnatin tarayya ta yi bayani kan ayyukanta.
Dino Melaye ya kira taron manema labarai
An ji ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026 a babban birni Abuja.
Dino ya ce majalisar na nuna alamun zama wani bangaren fadar shugaban kasa, maimakon kasancewa mai cin gashi da zaman kanta.
A cewarsa, dimokuradiyya na bukatar majalisa mai zaman kanta da za ta iya hana shugaban kasa wuce gona da iri wajen amfani da ikonsa.
Abin da Dino yake tsoro game da Tinubu
Sanatan ya ce damuwarsa ba wai Tinubu ya soke wa’adin mulkin shugaban kasa ko kuma yana shirin ci gaba da mulki har abada ba ne.

Kara karanta wannan
Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami
A maimakon haka, ya yi gargadi cewa raunin hukumomin da ya kamata su sa ido kan shugaban kasa na iya ba shi damar yin yadda ya so.
Punch ta rahoto shi ya ce hadn kai tsakanin majalisa da bangaren zartarwa yana da muhimmanci.
Sai dai ya nuna hakan bai kamata ya zama biyayya marar iyaka ba, ya kasance ana bin shugabanni ba tare da an iya taka masu burki ba.
A cewarsa, shugaban kasa na iya gabatar da dokoki, amma majalisa na da ikon nazari, gyara ko kin amincewa da su idan dai akwai bukata.
Misalin lokutan da majalisa ta ki yin aikinta
Dino ya kawo misalin gyaran dokar rundunar ’yan sanda da aka yi, yana ganin hakan ya ci karo da ka’idojin ritayar jami’an ’yan sanda.
‘Dan siyasar ya soki yadda majalisar ta gudanar da batun ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers a 2025, ya ce a nan ma an saba wa ka’ida.
Ya kuma soki yadda Majalisar Wakilai ta sake duba matsayarta kan dokar zabe ta 2026, yana ganin an rika yin gaba-da-baya a kai.
A batun kashe kudi, tshon sanatan ya nuna damuwa kan yadda majalisar ke sa ido kan aiwatar da kasafin kudi da kashe dukiyar gwamnati.
Bangaren taron manema labaran inda Dino Melaye ya soki majalisa yana shafinsa na Facebook.
Silar samun dukiyar Dino Melaye a duniya
An ji labari tsohon Sanatan Kogi, Dino Melaye ya bayyana cewa sayen akuya da ya yi tun yana dan shekara 12 ne ya zama silar dukiyarsa.
Ya yi ikirarin fara zuba jari a kamfanonin kasashen waje tun yana karami, kuma hakan ya taimaka masa wajen mallakar motoci 200 a yau.
Dino ya jaddada cewa bai taba satar dukiyar al'umma ko samun kwangilar gwamnati ba, ya ce bai taba samun gayyata daga EFCC ko ICPC ba.
Asali: Legit.ng

