Matsin tattalin arziki
Daya daga cikin attajiran Najeriya, Abdul Samad Rabiu, ya yi asarar dala biliyan 2.7, sakamakon garambawul da gwamnatin Najeriya ta yi a fannin kudin kasar.
Kungiyoyin kwadago da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC) sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 14.
Farashin Dala yana tashi kullum-yaumin kuma kudin Najeriya yana rasa darajarsa a kasuwa. EFCC ta fara cafke masu cin mutuncin Naira da karbar Daloli babu dalili.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta tabbatar da cafke Aisha Jibrin da wasu mutane 25 da ake zargi da hannu a zanga-zangar da aka yi a Minna, jihar Neja.
Sanata Ben Bruce ya ce a koma amfani da Glo domin kiran waya da hawa yanar gizo. Idan ba mu yi wadannan abubuwa uku ba, sai mu zo wata rana za a ji $1 za ta N5000.
Shugaba Bola Tinubu ya dawo gida lokacin da ake fama da tsadar rayuwa, lamarin da ya jawo zanga-zanga a wurare. Tinubu ya bada umarni tun daga Faransa kafin ya dawo.
Ministan tattali ya fadi tanadin da gwamnati tayi wa talaka a kan tsadar rayuwa. Wale Edun ya yi jawabi a lokacin da aka gayyace shi zuwa majalisar tarayya.
Za a ji yadda sabon tsarin CBN zai jawo karin tsadar kaya a Najeriya. Wani malamin makaranta kuma masanin tattalin arziki ya fada mana illar tashin farashin Dala.
Gwamnan Kano yana neman yadda farashin abinci zai sauko kafin watan azumi. Abba Kabir Yusuf ya yi alkawari zai raba abinci ga masu karamin karfi a kowace mazaba.
Matsin tattalin arziki
Samu kari