Abu 1 Tak da Gwamnati Ta Fadawa Kungiyoyin Kwadago da Zai Hana Su Shiga Yajin Aiki

Abu 1 Tak da Gwamnati Ta Fadawa Kungiyoyin Kwadago da Zai Hana Su Shiga Yajin Aiki

  • Gwamnatin tarayya ta magantu yayin da kungiyoyin kwadago na NCL da TUC suka tsunduma yajin aikin gargadi a Najeriya
  • Gwamnatin ta ba kungiyoyin hakuri tare da neman su janye wannan kudiri, tana mai alwashin cika alkawurran da ta daukar masu
  • Legit Hausa ta ruwaito maku cewa kungiyoyin kwadagon sun tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki 14 daga ranar Juma'a 9 ga wata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gwamnatin tarayya ta ba kungiyoyin kwadago na NLC da TUC tabbacin cewa za ta cika dukkan alkawurran da ta daukar masu a yarjejeniyar su ta 2023.

Ministar kwadago da samar da ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha ta ba da tabbacin a ranar Juma'a a wani taron manema labarai.

Kara karanta wannan

A karshe, ƙungiyoyin jihohi 19 sun bayyana matsayar Arewa kan mulkin Shugaba Tinubu

Gwamnati ta roki kungiyoyin kwadago su janye yajin aikin da suka shiga.
Gwamnati ta roki kungiyoyin kwadago su janye yajin aikin da suka shiga. Hoto: @nkeiruka_reps
Asali: Twitter

Onyejeocha ta shirya taron manema labaran ne don yin martani kan yajin aikin gargadi na kwanaki 14 da kungiyoyin suka shiga yau Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta sha alwashin cika alkawurran da ta dauka

Ta ce gwamnatin tarayya na iya bakin kokarin ta don ganin ta cika alkawurran da ta daukarwa kungiyoyin a ranar 2 ga watan Oktoba, 2023, rahoton The Nation.

Da wannan ta nemi kungiyoyin da su janye daga yajin aikin da suka tsunduma, tana mai cewa gwamnati na aiki tukuru don magance matsalolin kasar.

Ministar ta ce gwamnati ta fi son amfani da tsarin tattaunawa da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki a fadin duniya don samar da ci gaba a kasar.

Ta ce:

"Tabbas za mu cika dukkan alkawurran da muka daukarwa kungiyoyin kwadago, kuma ina da yakinin cewa shugaba Tinubu na tare da mutanen Najeriya a halin da suke ciki."

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Kwadago Sun Tsunduma Yajin Aiki a Fadin Najeriya Akan Wani Dalili 1 Tak

Da take tsokaci kan korafe-korafen da kungiyoyin kwadagon suka yi, Onyejeocha ta ce tuni gwamnati ta kammala shirin cika alkawarin kungiyoyin.

Gwamnati ta fara aiwatar da alkawurran da ta dauka

Sai dai ta ce akwai wasu alkawurran da hanyar gwamnatin ke nazari kan su don samar da hanyar aiwatar da su suma.

Ta ce:

"Tuni gwamnati ta aiwatar da karin albashin ma'aikata zuwa naira 35,000, sai dai mun samu korafin cewa akwai ma'aikatun da ba a kaddamar da hakan ba.
"Haka zalika yarjejeniya kan takaddamar da aka samu tsakanin kungiyar direbobi ta RTEAN da gwamnatin Legas shi ma an kawo karshensa."

Ta kuma yi nuni da cewa a bayan nan gwamnati ta kaddamar da wani kwamitin mutum 37 don duba yiwuwar kara albashi ga ma'aikata.

Haka zalika ministar ta ce akwai shirin shugaban kasa na fara amfani da iskar gas ta CNG don saukakawa 'yan kasar radadin janye tallafin fetur.

Kara karanta wannan

Mataimakin Bursar na jami'ar Kwara ya rasu yana kallon wasan Super Eagles da Afrika ta Kudu

NLC da TUC sun tsunduma yajin aikin gargadi

A jiya Alhamis, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa kungiyoyin kwadago na NCL da TUC sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 14.

Yajin aikin a cewar kungiyoyin zai zama gargadi ga gwamnati na gaza cika alkawurran da ta dauka a watan Oktoba 2023.

Yajin aikin ya fara ne daga rnar Juma'a 9 ga watan Fabrairu, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel