Hanya 1 Tak Da Gwamnati Tarayya Ta Dauka Don Karya Farashin Kayan Abinci, Ministan Yada Labarai

Hanya 1 Tak Da Gwamnati Tarayya Ta Dauka Don Karya Farashin Kayan Abinci, Ministan Yada Labarai

  • Gwamnatin tarayya ta ce ta dauki matakai don karya farashin kayan abinci a kasuwannin Najeriya tare da sa wa ya wadata
  • Ministan watsa labaran kasar ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce babban matakin da gwamnati ta dauka shi ne fitar da hatsi ga jama'a
  • Rahotanni sun bayyana cewa gwamnati ta ba da umurnin fitar da tan dubu 42 na shinkafa, gero da garri da sauran su don karya farashin su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ministan watsa labarai, Mohammed Idris, ya ce shirin da gwamnati ta yi ba fitar da hatsi zai karya farashin kayan abinci a kasuwanni.

A 'yan kwanakin nan farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali tare da yin zanga-zaga, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Ministan watsa labarai ya magantu kan matakin da gwamnati na dauka na karya farashin kayan abinci.
Ministan watsa labarai ya magantu kan matakin da gwamnati na dauka na karya farashin kayan abinci. Hoto: @HMMohammedIdris
Asali: Facebook

Daily Nigerian ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ba ministan noma umurnin fitar da tan dubu 42 na masara, gero da sauran kayan abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta fitar da kayan abinci

Da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, ministan ya ce fitar da hatsin zai sa abinci ya wada wanda kuma hakan zai karya farashin kayan abincin.

Ya ce:

"Gwamnatin Najeriya ta bullo da wasu tsare tsare da za su taimaka wajen karya farashin kayan abinci da kuma saka abincin ya wadata.
"Abu na farko da aka fara yi shi ne ba da umurnin fitar da tan dubu 42 na masara, gero, garri da sauran kayan abinci."

Gwamnati ta gana da kamfanonin sarrafa shinkafa

Mista Idris ya ce mataki na biyu da gwamnatin ta dauka shi ne ganawa da masu kamfanonin sarrafa shinkafa tare da basu umurni su bude rumbunansu.

Kara karanta wannan

Babban labari: CBN ya dakatar da ba gwamnatin tarayya bashi saboda dalili 1 tak

Ya ce:

"Sun shaida mana cewa za su iya fitar da tan dubu 60 na shinkafa, zuwa nan da makonni muna sa ran abincin ya wadata a ko ina."

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na duba yiyuwar shigo da wadannan kayan abincin idan har aka ga akwai bukatar hakan.

An cafke masu zanga-zagar matsin rayuwa a Neja

A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wacce ta jagoranci daruruwan mutane da yawansu mata ne wajen yin zanga-zaga a Neja, Aisha Jibrin tare da wasu mutum 24.

Rundunar ta ce A'isha ta yi ikirarin cewa ta jogoranci zanga-zagar ne domin nuna damuwarsu kan halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwar da ake ciki a kasar.

Sai dai rundunar ta ce wadanda suka yi zanga-zangar sun farmaki jami'ansu tare da lalata motocin sintiri na 'yan sandan da suka je don tabbatar da tsaro a wajen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel