Kungiyoyin kwadago sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya akan wani dalili 1 tak

Kungiyoyin kwadago sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya akan wani dalili 1 tak

  • Kungiyoyin kwadago na Najeriya da suka hada da kungiyar NLC da TUC sun shiga yajin aikin kwanaki 14 saboda tsadar rayuwa
  • Yajin aikin zai fara ne daga gobe Juma'a, 9 ga watan Fabrairu, don ba gwamnati damar cika alkawarin da ta daukarwa kungiyoyin
  • A cikin wata sanarwa, kungiyoyin sun yi ikirarin cewa gwamnati taki waiwayar yarjejeniyar da suka yi a watan Oktoba 2023

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kungiyoyin kwadago da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC) sun fitar da sanarwar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 14.

Yajin aikin kamar yadda majalisun zartarwar kungiyoyin suka bayyana zai fara ne daga gobe Juma'a, 9 ga watan Fabrairu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

A karshe, ƙungiyoyin jihohi 19 sun bayyana matsayar Arewa kan mulkin Shugaba Tinubu

Kungiyoyin kwadago sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya.
Kungiyoyin kwadago sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Getty Images

Kungiyoyin sun zargi gwamnatin tarayya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana cewa ba a aiwatar da yarjejeniyar mai dauke da abubuwa 16 da aka cimma a ranar 2 ga watan Oktoban 2023 tsakanin su da gwamnatin tarayya ba.

Kungiyoyin sun koka kan matsin tattalin arziki

Shugabannin kungiyoyin TUC da NLC na kasa sun bayyana bakin cikin su kan yadda gwamnati ta nuna halin ko in kula da wahalhalun da al’umma ke ciki.

Kungiyoyin a cikin wata sanarwa kamar yadda The Nation ta wallafo sun ce:

“Yarjejeniyar ta mayar da hankali ne kan magance dimbin radadin da jama'a ke fama da shi musamma kan tsarin IMF/WB da ya jawo tashin farashin fetur da kuma faduwar darajar Naira.
Wadannan tsare-tsare guda biyu, kamar yadda muka yi hasashe, sun yi mummunar illa ga tattalin arzikin talakawa da ma’aikatan Najeriya.”

Kara karanta wannan

Mataimakin Bursar na jami'ar Kwara ya rasu yana kallon wasan Super Eagles da Afrika ta Kudu

NLC da TUC sun ba gwamnati wa’adin kwanaki 14

Suka kara da cewa:

“Abin takaici ne yadda aka tilasta mana daukar irin wadannan matakan, amma rashin kula da jin dadin ‘yan kasa da ma’aikatan Najeriya da kuma tsananin wahalhalu ya sa ba mu da wani zabi.
"Ma’aikatan Najeriya da ‘yan kasa, NLC da TUC sun ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 daga gobe 9 ga Fabrairu su aiwatar da alkawurran da suka dauka.”

An rantsar da sabbin mambobin majalisar tarayya su 12

A wani labarin, kakakin majalisar tarayya, Tajudeen Abbas ya rantsar da sabbin mambobin majalisar su 12 da INEC ta ba takardar shaidar cin zabe.

An ruwaito cewa akwai ragowar mambobi biyu da ba a rantsar da su ba, sannan akwai jihohi biyu da INEC ke kokarin kammala zaben su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel