Bayan Dangote, Shima Abdul Samad BUA Ya Yi Asarar Dala Biliyan 2.7, an Gano Dalili

Bayan Dangote, Shima Abdul Samad BUA Ya Yi Asarar Dala Biliyan 2.7, an Gano Dalili

  • An ruwaito cewa hamshakin dan kasuwar Najeriya, Abdul Samad Rabiu ya tafka asarar dala biliyan 2.7
  • Hakan kuwa ya faru ne sakamakon karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi a wani yunkuri na farfaɗo da tattalin arziki
  • Wannan asarar biliyoyin daloli da hamshakin dan kasuwar ya yi, ya sa shi komawa zuwa 448 a jerin masu kudin duniya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Hamshakin dan kasuwar Najeriya, shugaban rukunin kamfanonin BUA, ya yi asarar dala biliyan 2.7 a cikin dan karamin lokaci.

Abdul Samad Rabiu ya yi asarar wadannan makudan kudaden ne biyo bayan karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi a yunkurin farfado da tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Mataimakin Bursar na jami'ar Kwara ya rasu yana kallon wasan Super Eagles da Afrika ta Kudu

Abdul Samad BUA ya yi asarar dala biliyan 2.7. Hoto
Abdul Samad BUA ya yi asarar dala biliyan 2.7. Hoto: @BUAgroup
Asali: Getty Images

Rabiu, wanda arzikin sa ya haura dala biliyan 8.4 a watan Janairu, yanzu shi ne na 448 a jerin masu kudin duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamba biyu a jerin masu kudin Najeriya, Abdul Samad Rabiu ya tafka babbar asara a yayin da Najeriya ta karya darajar kudinta karo na biyu a cikin wata 8.

Hamshakin dan kasuwar ya tafka asarar naira biliyan 2.7 a wani yunkuri da gwamnatin kasar ka yi na farfaɗo da tattalin arziki.

Arzikin da Rabiu ya mallaka ya koma dala biliyan 5.7

Rahoton mujallar Forbes ya nuna cewa kudin da Rabiu ya mallaka a yanzu ya koma dala biliyan 5.7 daga dala biliyan 8.4 da ya mallaka a watan Janairu 2024.

Faduwar arzikin nasa ne ya zo ne a faduwar darajar Naira da ta yi akan Dalar Amurka, lamarin da ya ja hamshakin mai kudin ya sauka kasa a jerin masu kudin duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN da ministocin Tinubu 2 sun bayyana a gaban majalisa, sun yi bayanai masu muhimmanci

Hakazalika, karya darajar Naira ya shafi farashin simitin BUA da kayan masarufi da kamfanin ke sarrafawa.

Idan baku manta ba, a makon da ya gabata mun ruwaito muku yadda attajirin nahiyar Afrika Aliko Dangote ya tafkar biliyoyi.

Mark Zuckerberg ya shiga gaban Bill Gates a yawan dukiya

A wani labarin kuma, mamallakin kamfanin Meta, Mark Zuckerberg ya shiga gaban attajiri Bill Gates a sahun masu kudi na duniya.

Hakan na zuwa ne bayan da Zuckerberg ya samu ribar dala biliyan 36, wanda ya ba shi damar komawa na hudu a jerin masu kudin duniyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel