Zanga-Zanga Ta Tada Hankalin Gwamnati, Shugaban Kasa Ya Dauki Mataki a Guje

Zanga-Zanga Ta Tada Hankalin Gwamnati, Shugaban Kasa Ya Dauki Mataki a Guje

  • Shugaban kasar Najeriya ya bada umarni a magance matsalar abinci da mutane suka fara nuna fushinsu
  • Bola Tinubu ya dawo gida lokacin da ake fama da tsadar rayuwa, lamarin da ya jawo ake zanga-zanga
  • Jam'iyyar APC tana zargin 'yan adawa suna da hannu a zanga-zangar da aka shirya a makon nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Zanga-zangar da mutane suka shiya a makon nan ya firgita gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da aka zaba a 2023.

A babban birnin Neja watau Minna, mutane sun yi zanga-zanga a kan tsadar abinci, Premium Times ta kawo karin rahoto.

Bola Tinubu
An fara yi wa Bola Tinubu zanga-zanga Hoto: Asiwaju Bila Ahmed Tinubu/Getty
Asali: Facebook

Gwamnatin Tinubu ta zabura

Wannan mataki da jama’a su ka dauka a sakamakon kuncin rayuwa da aka shiga bai yi wa gwamnatin Bola Tinubu dadi ba.

Kara karanta wannan

Yadda jami’an yan sanda suka yi garkuwa da wani mazaunin Abuja, suka kwashe gaba daya kudin asusunsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin haka shugaban kasa ya bada umarnin gaggawa cewa jami’an gwamnati suyi kokarin magance wannan matsalar.

Jawabin Ministan labarai

Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris Malagi ya sanar da haka bayan an yi wani taro a Abuja.

Malagi wanda daga jihar Neja da aka yi zanga-zangar ya fito, ya ce karanci da tsadar abinci a yau yana damun Bola Tinubu.

“Gwamnatin nan ta damu sosai game da halin da ‘yan Najeriya su ke ciki, musamman abin da ya faru jiya (Litinin) a Minna.
“Saboda haka gwamnati ta dauki wasu matakai domin ganin mutanen Najeriya sun samu sauki ta bangaren samun abinci.”

- Muhammad Idris

Kwamitin da Shugaba Tinubu ya kafa

Kwamitin da ke da alhakin samar da abinci cikin gaggawa zai cigaba da yin zama har zuwa Alhamis domin a kawo mafita.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tono tushen matsalar ƴan bindiga a Arewa, ya jero hanyoyin magance su

‘Yan kwamitin sun hada da Femi Gbajabiamila, Yemi Cardoso, Wale Edun, Nuhu Ribadu sai Abubakar Kyari da Atiku Bagudu.

NAN ta ce ragowar su ne: Sanata Aliyu Sabi Abdullahi da Dr. Mariya Mahmoud Bunkure wadanda kananun ministoci ne.

Minista ya jero kokarin gwamnatin Tinubu

A aikin kwamitin akwai duba yadda za a fito da abinci daga rumbunan kasa kamar yadda aka saba idan an shiga halin yunwa.

Rahoton ya ce gwamnati ta fara magana da masu casa da manyan ‘yan kasuwa domin su fito da abincin da ke hannunsu.

Ministan labaran yake cewa gwamnati za ta kawowa talakawa saukin yadda za a koshi.

Shugaban kasa ya dawo daga waje

Mai girma Bola Ahmed Tinubu wanda ya bar Najeriya a watan Junairu ya iso Abuja a daren yau kamar yadda aka samu labari dazu.

Manyan jami’an gwamnati da wasu gwamnoni suka tarbo shugaba Tinubu a filin jirgi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel