Ramadan: Abba Ya Zauna da ‘Yan Kasuwan Kano, Ya Roki a Fito da Abincin da Aka Boye

Ramadan: Abba Ya Zauna da ‘Yan Kasuwan Kano, Ya Roki a Fito da Abincin da Aka Boye

  • Abba Kabir Yusuf ya kira zama na musamman da kungiyoyin ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki
  • Gwamnan jihar Kano ya lallabi ‘yan kasuwa su tausayawa jama’a, su fito da kayan da suka boye
  • Abba ya yi alkawarin raba abinci ga masu karamin karfi a duk mazaban kananan hukumomin Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Mai girma Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi kira da ‘yan kasuwa su guji boye abinci a lokacin da ake cikin kunci.

Abba Kabir Yusuf ya roki ‘yan kasuwan su fito da ainci su saidawa al’umma, Gwamnan ya tabbatar da hakan a shafin X.

Abba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf da 'yan kasuwan Kano Hoto: @KYusufAbba
Asali: Twitter

Ganin watan azumi yana karasowa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya kira taro da kungiyoyi na ‘yan kasuwa a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Talaka zai ji a jikinsa sakamakon tashin kudin shigo da kaya da aka yi wa Kwastam

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A taron ne aka fahimci Abba Yusuf zai nemi ya zauna da Bola Ahmed Tinubu kan lamarin.

Abba ya koka kan tsadar kaya a Kano

Legit Hausa ta tattaro Abba yana mai cewa yadda farashin abinci da sauran kaya suke tashi a kasuwanni a halin yanzu abin tsoro ne.

Gwamnan yake cewa al’umma su na shan matukar wahala, dole a dauki mataki.

Kwamishinan kasuwanci na Kano, Alhaji Abbas Sani Abbas ya ce taron da gwamnan ya yi da ‘yan kasuwa ya zo lokacin da ya dace.

Alhaji Abbas Sani Abbas ya ce gwamnatin NNPP tana neman kawowa al’umma sauki. Nan da wata guda za a fara azumi a duniya.

Gwamna ya Abba ya ce rayuwa tayi wahala

Gwamnatin Kano ta koka a kan yadda kananan ma’aikata da masu karamin karfi su ke wahala, don haka za a raba abinci a ko ina.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya caccaki Abba Gida Gida kan shirinsa na ganawa da Tinubu

Abba ya sanar da cewa baya ga kokarin ganin farashi ya sauko kafin azumi, za ayi rabon kayan abinci a duka mazabu 484 na Kano.

Wasu na sukar gwamnatin Abba

Hassan Sani Tukur wanda hadimi ne ga gwamnan na Kano ya maidawa irinsu Bashir Ahmaad martani da ke sukar yunkurin.

A dandalin X, Hassan Sani Tukur ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari da Bashir ya yi wa aiki ta haifar da matsin lambar da ake ciki.

APC v NNPP a siyasar Kano

Kwanaki aka ji labari Ibrahim Shekarau ya soki gayyatar da Abdullahi Ganduje ya aikawa wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ta shiga APC.

Tsohon gwamnan ya yi nuni da cewa matakin da shugaban na APC ya ɗauka bai kamata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel