Talaka Zai Ji a Jikinsa Sakamakon Tashin Kudin Shigo da Kaya Da Kwatsam Ta Yi

Talaka Zai Ji a Jikinsa Sakamakon Tashin Kudin Shigo da Kaya Da Kwatsam Ta Yi

  • Gwamnatin tarayya ta lafta kudin da kwastam ta ke karba wajen shigo da kaya daga kasashen waje
  • Sau biyu aka yi karin a cikin awa 24, hakan ya birkita ‘yan kasuwan da ke sayo kayansu a ketare
  • Wani malamin makaranta kuma masanin tattalin arziki ya fada mana yadda tsarin zai taba Najeriya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kwastam tayi karin kudin shigo da kaya daga ketare sau biyu a cikin kwana guda, wannan yana da tasiri ga tattalin arziki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kaya za su kara tsada a dalilin canjin farashin shigo da kaya daga kasar waje da gwamnati ta yi.

Tsadar CBN
CBN ya jawo kaya za su tashi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Darajar Dalar Amurka a CBN

Kara karanta wannan

Mataimakin Bursar na jami'ar Kwara ya rasu yana kallon wasan Super Eagles da Afrika ta Kudu

Sauyin ya zama dole ne ganin yadda babban bankin Najeriya na CBN ya tashi farashin Dala daga N953 a Janairu zuwa N1, 356.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin a je ko ina sai farashin kudin Amurkan ya karu da N57, ya lula zuwa N1,413.62.

Daily Trust ta ce kungiyar MAN ta yi tir da sabon tsarin, ta ce kaya za su kara tsada musamman ga su da ke zuwa kasar waje.

Me tsarin yake nufi ga tattalin arziki?

Tijjani Ahmad masani ne a kan harkar tattalin arzikin kasa, Legit Hausa ta tuntube shi domin jin tasirin da wannan canji zai yi.

Masanin tattalin ya shaida mana tashin farashin zai taba ‘yan kasuwa, talakawa da gwamnati domin an dogara da kayan ketare.

Da farko kayan waje za su kara tsada, a sakamakon haka mutane za su fara kaurace masu wanda haka zai haifar da rashin ciniki.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala

Malam Tijjani Ahmad ya nuna rashin cinikin masu saida irinsu kayan wuta, na’urori, abubuwan hawa da tufafi zai yi ila ga tattali.

Gwamnatin tarayya za ta samu kudi

Yayin da masu sayen kaya da ‘yan kasuwa za su yi wayyo Allah da tsarin, watakila gwamnatin kasar ta samu karin kudin shiga.

Idan baitul-mali ya cika za a iya yi wa talakawa aiki, sai dai masanin ya ce rashin ciniki da kasashe zai iya damalmala dangantaka.

Yadda za a farfado da tattalin Arewa

Ana da labari Muazu Magaji ya wanke Bola Tinubu, ya zargi Muhammadu Buhari da jefa al’umma cikin matsin lambar tattalin arziki.

Dansarauniya yana so attajiran Arewa irinsu Aliko Dangote su kafa bankuna da za su maida hankali a rage talaucin da ke yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng