Gwamnoni ga Tinubu: Ga Hanyar Shawo Kan Matsalar Tsadar Abinci da Tattalin Arziki
- Kungiyar NGF tayi zaman farko a shekarar 2024, an tattauna a kan matsin lambar tattalin arziki
- Gwamnoni sun gamsu akwai matsalolin tsadar abinci, tashin darajar Dala da rashin tsaro a kasar nan
- A karshen taron, gwamnonin sun gabatar da shawarwari da matakan da suka dauka a jihohinsu
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Kungiyar NGF ta gwamnonin Najeriya ta ce akwai bukatar a magance matsalar tsadar kayan abinci da karyewar Naira.
The Cable ta rahoto gwamnonin jihohin kasar su na cewa ya kamata Bola Ahmed Tinubu ya yi kokarin inganta tsaro a Najeriya.

Asali: Twitter
Taron NGF a kan tsaro, abinci da tattali
Gwamnonin sun bayyana matsayarsu ne a jawabin bayan taro da su ka fitar a ranar Talata bayan sun yi wani zama na gaggawa.

Kara karanta wannan
Sarkin Musulmi da Kiristoci Sun Hada Kai, Sun Taso Gwamnati Gaba Kan Tsadar Rayuwa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wannan zama da aka yi ta yanar gizo, gwamnonin jihohin sun kawo shawarwarin yadda za a samu sauki a cikin kankanin lokaci.
Wannan shi ne zaman farko da kungiyar NGF ta gwamnoni tayi tun da aka shiga 2024.
Shugaban kungiyar kuma Mai girma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya sa hannu a madadin sauran takwarorinsa.
Gwamnoni sun bada sirrin samun Dala
Gwamnonin sun ce dole a san yadda Najeriya za ta rage dogara da kudi da kayan kasashen waje da duk wasu ayyuka na ketare.
Independent ta ce kungiyar NGF ta bada shawarar a saukaka ka’idojin fita da kaya zuwa kasashen waje domin a samu kudin ketare.
Idan ana neman saukin kuncin da aka shiga, gwamnonin sun ce zai yi kyau a toshe kafar fita da albakartun kasa ta barauniyar hanya.

Kara karanta wannan
Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala
Wata shawarar kuma ita ce a kara adadin gangunan danyen man da ake hakowa a rana.
Za a yaye tsadar kayan abinci
A game da tsadar kayan abinci, gwamnonin sun amince su fito da tsare-tsaren tallafi na gaggawa domin ayi maganin yunwa a jihohi.
Gwamnonin za su hada kai da ‘yan kasuwa kuma za a fito da abincin da aka boye a rumbuna domin a iya karya farashinsu a kasuwa.
Tinubu ya bada umarni a saki abinci
Ganin halin da aka shiga na tsada da yunwa, a jiya aka samu rahoto Mai girma Bola Tinubu ya ce a fito da kayan abincin da aka adana.
Ministan labarai ya sanar da matsayar da aka cin ma bayan zaman su a fadar Aso Villa.
Asali: Legit.ng