Tsadar Rayuwa: Dandazon Matasa Sun Gudanar da Zanga-Zanga a Jihar PDP

Tsadar Rayuwa: Dandazon Matasa Sun Gudanar da Zanga-Zanga a Jihar PDP

  • Wasu matasa a Osogbo, babban birnin jihar Osun suna zanga-zanga akan matsin tattalin arziki da rashin tsaro a Najeriya
  • Masu zanga-zangar sun ce ba za su lamunci matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar ba saboda 'yan Najeriya basu cancanci shan wahala ba
  • Matasan sun bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wani abu domin inganta rayuwar al'umma

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Osogbo, jihar Osun - Tsadar rayuwa da ake fama da ita ta tunzura wasu matasa zuwa ga yin zanga-zangar lumana a hanyar MDS da ke garin Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, matasan na ta wakoki dauke da kwalayen rubutu iri-iri suna masu nuna gajiyawarsu saboda matsin rayuwa.

Kara karanta wannan

"Ku Riƙa Faɗin Alheri Kan Kasar Ku" Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga 'yan Najeriya

Matasa sun yi zanga-zanga saboda tsadar rayuwa
Tsadar Rayuwa: Dandazon Matasa Sun Gudanar da Zanga-Zanga a Jihar PDP Hoto: @BishopPOEvang
Asali: Twitter

Masu zanga-zangar sun yi kira ga gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu akan ta gaggauta daukar mataki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin rubutun da ke rubuce jikin kwalayen sun hada da 'ka sauya manufofin marasa dadi', ''yan Najeriya na shan wahala, ba za mu iya ci gaba a haka ba', da 'Mu mutane ne, a daina azabtar da 'yan kasar', da dai sauransu.

Mun gaji da matsin rayuwa, matasan Osun

Shugaban masu zanga-zangar, Waheed Lawal, wanda ya yi jawabi ga masu zanga-zangar ya ce wahalar da ake ciki ba shine sabonta atan da Shgugaba Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya alkawari ba a yayin kamfen dinsa, Channels TV ta ruwaito.

Lawal ya ce dole gwamnatin Tinubu ta yi wani abu game da wahalar da mutane ke sha.

Ya ce:

"'Yan Najeriya sun cancanci rayuwa mai inganci. Sun yi mana alkawarin sabunta ata amma abin da suke ba mu a yanzu shine sabon wahala.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai kazamin hari jihar Arewa, sun sheke mutum 6 da sace mata 20

"Mun yi watsi da sabunta wahalhalu a rayuwarmu, da tattalin arzikinmu saboda ’yan Najeriya sun cancanci ingantacciyar rayuwa.
"Abin da 'yan Najeriya ke so shine zaman lafiya. Ba ma son rashin tsaro a kasarmu kuma. Ba za mu iya tafiya daga Osogbo zuwa Ibadan ba tare da fargaba ba. Za ka dunga tunanin za su yi garkuwa da kai."

Ya ci gaba da cewa:

"Mun fara wannan fafutukar a yau kuma idan gwamnati ta ki sauraron mu, za mu ci gaba da tattar mutanenmu don yi zanga-zangar wannan wahalar saboda ya ishe mu haka."

Malaman addini sun magantu kan tsadar rayuwa

A wani labarin, mun ji cewa jagororin addinin musulunci da kiristanci a Najeriya, sun yi kira ga hukumomi su samar da abinci ga talakawa.

Wani rahoton Daily Trust ya ce masana addinin sun yi wannan kira a ranar Alhamis, su ka koka cewa jama’a suna shan wahala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel