An Damalmala Tattali Kafin Mayun 2023, Tinubu Ya Ceci Najeriya Inji Ministan Kudi

An Damalmala Tattali Kafin Mayun 2023, Tinubu Ya Ceci Najeriya Inji Ministan Kudi

  • Wale Edun ya yi jawabi a lokacin da shi da wasu jami’an gwamnatin Najeriya su ka je majalisa
  • Ministan kudin yana cikin wadanda ‘yan majalisa su ka gayyata domin jin kokarin da suke yi
  • Ana cikin matsin tattalin arziki, Edun ya nuna duk halin da ake ciki, an samu cigaba a kan bara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun yana da ra’ayin an kama hanyar kawo gyara da Bola Ahmed Tinubu ya karbi iko.

Wale Edun ya yi ikirarin cewa zuwan Mai girma Bola Ahmed Tinubu a watan Mayu, ya hana a shiga masifa, Channels ta kawo rahoton.

Tinubu
Wale Edun ya ce Bola Tinubu ya ceci kasa Hoto: @Dolusegun16, Getty
Asali: Twitter

Majalisa ta dauki mataki a kan halin tattali

Ministan tattalin arzikin ya yi wannan bayani ne da ya bayyana gaban ‘yan majalisar wakilan tarayya domin ya yi masu karin haske.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fito karara ya fadawa Atiku yadda ya samu Najeriya daga hannun Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Inda mu ke a yanzu ta fuskar tattalin arzikin kasa ya fi inda mu ke a ranar 29 ga watan Mayun 2023.”
"Mun saurari gwamnan bankin CBN. (Cordoso) ya yi magana a kan muhimmancin daurewa a kan haka."

- Wale Edun

Gwamnatin Tinubu ta ceto tattali?

Kafin Bola Tinubu ya kawo manufofinsa takwas, Edun ya ce kasar ta kama hanyar da ba ta bullewa, ana gabar aukawa tashin hankali.

Ministan ya shaidawa ‘yan majalisa cewa kafin su shigo ofis, akwai facaka a tsarin da gwamnatin tarayya ta ke bi wajen kashe kudi.

Ministan Tinubu ya yarda ana jin jiki

Punch ta ce Ministan ya gamsu cewa al’umma sun shiga mawuyacin hali a Najeriya, ya kuma sha alwashin za a magance matsalar.

Edun ya ce Mai girma Bola Tinubu da gaske yake yi wajen ganin rayuwa tayi wa kowa sauki sakamakon kuncin da ake burma.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN da ministocin Tinubu 2 sun bayyana a gaban majalisa, sun yi bayanai masu muhimmanci

"Farashin kaya sun tashi, rayuwa ta kara wahala kuma tun farko shugaban kasa da gaske yi ya ga cewa ba a bar talaka a baya ba."

- Wale Edun

A dalilin kuncin da ake fama da shi da tsadar rayuwa bayan an cire tallafin fetur da kawo wasu tsare-tsare, Edun ya ce an raba kaya.

Tinubu: Tattalin arzikin kasar nan a 2023

An rahoto Bayo Onanuga yana cewa shugaba Bola Tinubu ya gaji tattalin arziki mai rauni, wanda dole yana bukatar ayi garambawul.

Hadimin shugaban kasar ya ce a kasafin 2023 da Tinubu ya iske ya nuna 97% na kudin da aka samu zai tafi ne wajen biyan bashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel