Tsadar Rayuwa: Yan Sanda Sun Cafke Aisha Jibrin da Mutane 24 da Suka Jagoranci Zanga-Zanga a Minna

Tsadar Rayuwa: Yan Sanda Sun Cafke Aisha Jibrin da Mutane 24 da Suka Jagoranci Zanga-Zanga a Minna

  • Rundunar 'yan sanda ta cafke wadanda suka jagoranci zanga-zagar daruruwan mutane a jihar Neja wanda ya jawo tashin hankali
  • A ranar Litinin ne Aisha Jibrin tare da wasu suka jagoranci daruruwan mata da maza da sunan yin zanga-zaga kan tashin farashin kayan abinci
  • Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Neja ta ce masu zanga-zagar sun farmaki jami'ansu tare da lalata motoci da haddasa cunkoso a babban titi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Neja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta tabbatar da cafke wasu mutane 25 da ake zargi da hannu a wata zanga-zanga da aka yi a Minna, jihar Neja.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa a ranar Litinin ne masu zanga-zangar suka tare hanyar Minna-Bada da kuma titin Kpakungu don nuna adawa da tashin farashin kayan abinci.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga sun tada hankalin Gwamnati, Shugaban kasa ya dauki mataki a guje

Yan sanda sun kama Aisha Jibrin da wasu mutane 24 a Neja.
Yan sanda sun kama Aisha Jibrin da wasu mutane 24 a Neja. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

An kama jagororin zanga-zangar da aka yi a Neja

Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya ce rundunar ta kama wadda ta jagoranci zanga-zangar, Aisha Jibrin tare da wasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Za a iya tunawa cewa a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu da misalin karfe 7 na safe, mata da maza sun hada kansu tare da tare hanyar Minna zuwa Bida da kuma shatale-talen Kpakungu.
"Sun yi ikirarin cewa suna zanga-zangar nuna adawa da karin farashin kayan abinci, wanda ya haifar da cunkoso a babbar hanyar garin."

Masu zanga-zangar sun farmaki jami'an 'yan sanda

Abiodun ya ce masu zanga-zagar sun ki sauraron duk wani roko da mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar, DCP Shehu Umar Didango ya yi.

"Hatta mataimakin gwamnan Neja, Yakubu Garba sai da ya lallashe su amma a karshe suka so mayar da abun ya koma tashin hankali.

Kara karanta wannan

Mata sun barke da zanga-zanga saboda mazansu ba su kusantarsu idan dare ya yi, sun fadi dalili

"Jami'an rundunar sun yi kokarin tarwatsa masu zanga-zagar cikin lumana amma suka farmake su ta hanyar jifa da duwatsu, kwalabe, adduna da sauransu tare da lalata motocin 'yan sandan."

Kakakin rundunar ya kara da cewa, an cafke Aisha Jibrin, Fatima Aliyu, Fatima Isyaku, dukkan yan yankin Soje "A" wadanda suka jagoranci zanga-zangar.

Za a gurfanar da Aisha da mutane 24 gaban kotu

A cewar Mr Abiodun, daga cikin abubuwan da aka kwato akwai tebura da itatuwa da aka tare hanyoyi da su, sai adduna, almakashi, wukake da sauran kananun makamai.

"Sai dai ita Aisha ta yi ikirarin cewa ba ta da masaniyar jagorantar daruruwan mata da 'yan daba zai iya haifar da tarzoma inda ta ce sun yi kokarin sanar da 'yan sanda amma ba su yi ba."

A cewar Mr Abiodun.

Ya kuma bayyana cewa za a gurfanar da mutane da aka kama gaban kotu da zaran rundunar ta kammala bincike.

Kara karanta wannan

Yadda jami’an yan sanda suka yi garkuwa da wani mazaunin Abuja, suka kwashe gaba daya kudin asusunsa

Gobara ta yi ajalin wani yaro dan shekara 4 a jihar Kano

A wani labarin, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce wani yaro dan shekara 4 ya gamu da ajalinsa bayan da gobara ta tashi a cikin ginin da ya ke ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa yaron na wasa da ashana wanda ya yi silar kamawar wutar, a gidan su da ke unguwar Yakasai a birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel