Najeriya Za Ta Kashe Dala Biliyan 11.6 wajen Biyan Bashin Kasashen Ketare a 2026

Najeriya Za Ta Kashe Dala Biliyan 11.6 wajen Biyan Bashin Kasashen Ketare a 2026

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce kusan rabin kudaden shiga na Najeriya a 2026 za su tafi ne wajen biyan basussukan da ake bin kasar
  • Ya koka kan yadda tsarin hada-hadar kudin duniya ke hana kasashen Afirka samun rancen da ya dace domin bunkasa masana’antun su
  • Shugaban Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron Africa Forward Summit da aka gudanar a Nairobi, kasar Kenya, ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya za ta kashe d'Dala biliyan 11.6 wajen biyan bashin kasashen waje a shekarar 2026.

Adadin ya nuna kari sosai idan aka kwatanta da Dala biliyan 5.21 da kasar ta ware wajen biyan bashin kasashen waje a shekarar 2025 kamar yadda bayanan babban bankin Najeriya suka nuna.

Kara karanta wannan

Albishir: Najeriya za ta kaddamar da sabon tsarin watsa shirye shiryen talabijin

Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a taron kasashen Afirka da ya halarta a birnin Nairobi na kasar Kenya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron Africa Forward Summit da aka gudanar a Nairobi, kasar Kenya, ranar Talata.

Tinubu ya koka kan biyan basussuka

A cewar shugaban kasar, kusan rabin kudaden shiga da Najeriya ke sa ran samu a shekarar 2026 za su tafi ne wajen biyan basussuka karkashin tsarin hada-hadar kudin duniya na yanzu.

Ya ce duk wata Dala da kasar ke kashewa wajen biyan kudin ruwa mai tsada na rage damar zuba jari a muhimman bangarorin tattalin arziki.

“Duk wata Dala da ta fita daga baitul malinmu domin biyan kudin ruwa mai tsanani, mun yi asarar amfani da ita a bangaren karafa, masana’antar yadi, sarrafa kayan gona ko harkokin fasahar zamani.
“Dala ce da ba ta taimaka wajen horas da matashin injiniyan Najeriya ko samar da lantarki mai sauki ga masana’antunmu ba," in ji Tinubu.

Tinubu ya soki tsarin hada-hadar kudi

Kara karanta wannan

An saki sunayen kananan hukumomi 3 da Boko Haram ta tilasta wa biyan haraji a Yobe

Tinubu ya ce kasashen Afirka na fuskantar matsala daga masu bayar da bashi, wadanda ke kallonsu a matsayin kasashe masu hadari wajen biyan bashi, duk da gyare-gyaren tattalin arzikin da suka aiwatar.

Ya ce tsarin hada-hadar kudin duniya na yanzu na kawo cikas ga kokarin Afirka na bunkasa masana’antu saboda wahalar samun jari mai saukin ruwa.

“Ta yaya masana’anta a Afirka za ta yi gogayya da takwararta a Turai, Asiya ko Arewacin Amurka yayin da kudin ruwa a kasashenmu ya ninka nasu sau biyar zuwa goma?” Tinubu ya tambaya.
Afirka.
Alhaji Aliko Dangote, AbdulRahman Rabiu BUA da wasu manyan yan kasuwa a taron Afirka da ya gudana a kasar Kenya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Abin da kassshen Afirka ke bukata

Tinubu ya ce Najeriya da sauran kasashen Afirka ba taimako suke nema daga duniya ba, illa tsarin hada-hadar kudin da zai bai wa nahiyar damar bunkasa masana’antu.

Ya ce Afirka na son tsarin da zai ba ta damar sarrafa ma’adananta, tace danyen mai, kera magunguna da kuma yin gogayya daidai da sauran kasashen duniya, kamar yadda Leadership ta kawo.

Shugaba Tinubu zai daina ciyo bashi?

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Abmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai daina karbo wa Najeriya bashin kudi ba matukar akwai bukatar hakan.

Kara karanta wannan

Atiku ya 'bankado' shirin gwamnoni game da tazarcen Tinubu a zaben 2027

Tinubu ya ce maimakon sukar ciyo bashi da yan Najeriya ke yi, kamata ya yi a hada kai domin yin aiki tukuru da zai ba da damar biyan wadannan kudade.

A ranar 15 ga Afrilu, Hukumar Kula da Basussuka (DMO) ta bayyana cewa jimillar bashin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.27 a karshen zangon karshe na shekarar 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262