Kungiyoyin Jihohin Arewa 19 Sun Faɗi Wanda Ya Jawo Tsadar Rayuwa Tsakanin Buhari da Tinubu
- Wasu kungiyoyin Arewa sun yi jan hankali ga malamai da 'yan siyasa daga yankin game da gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu
- Kungiyoyin masu muradin kare damokradiyyan sun ce 'yan siyasar Arewa basu yi wa gwamnatin Tinubu adalci ba da har suka fara ganin ta gaza tun ba a kai ko'ina ba
- A cewarsu, gwamnati mai ci ta gaji tarin matsaloli ne daga wajen tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yake 'dan Arewa ne
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Wasu gamayyar kungiyoyi na jihohin Arewa 19, sun bukaci 'yan siyasa daga yankin masu kushe kokarin gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da su daina.
Kungiyoyin masu muradin kare damokradiyya, sun dauki wannan matsayin ne a karshen taronsu da ya gudana a Abuja domin nazarin halin da kasar ke ciki, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Shugaban kungiyar, Shehu Abdullahi Ma’aji, ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa da malamai daga yankin Arewa sun yi gaggawa wajen watsi da gwamnatin Tinubu a matsayin wacce ta gaza, 'yan watanni da hawansa karagar mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aji ya ce 'yan siyasar Arewa basu yi wa gwamnatin Tinubu adalci ba, cewa ta gaji tarin matsaloli daga wanda ya gabace ta, wato gwamnatin Muhammadu Buhari, rahoton Daily Post.
Ya kuma bayyana cewa sun yanke shawarar yabawa 'yan Arewa masu kishin kasa da daukacin 'yan Najeriya da ke ba gwamnati mai ci goyon baya a kokarinta na samar da mafita ga matsalolin da ke addabar al'umma.
Kungiyoyin Arew sun fadi makarkashiyar da ake yi wa gwamnatin Tinubu
Kungiyoyin sun kuma zargi wasu da suka kira da 'yan siyasa marasa kishin da mayar da hankali wajen tunzura talakawa a kan gwamnati.
Hakazalika, sun yi nuni ga cewa matsalolin da Shugaba Tinubu ya gada daga gwamnatin Muhammadu Buhari ba abu ne za a iya magance su a lokaci guda ba sai sannu a hankali.
Kungiyar ta kuma yi zargin cewa akwai wata kungiya da 'yan siyasa ke kokarin amfani da ita domin gudanar da gagarumin zanga-zanga a fadin kasar domin bata sunan wannan gwamnati.
Matasa sun yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa
A wani labarin, mun ji cewa tsadar rayuwa da ake fama da ita ta tunzura wasu matasa zuwa ga yin zanga-zangar lumana a hanyar MDS da ke garin Osogbo, babban birnin jihar Osun.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, matasan na ta wakoki dauke da kwalayen rubutu iri-iri suna masu nuna gajiyawarsu saboda matsin rayuwa.
Asali: Legit.ng