Muhammadu Buhari
Najeriya ta yi sabon shugaban ƙasa bayan an rantsar da Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin sabon shugaban ƙasa. Kafin Tinubu Najeriya ta yi shugabanni da yawa.
Shugaba Buhari ya ce ya matsu ya koma Daura da ke jihar Katsina bayan ya gama mulkinsa a yau Litinin 29 ga watan Mayu, ya ce zai koma ne don kula da dabbobinsa.
Ana yin jawabin rantsar da sabon shugaban kasa ko zababben shugaban kasa a karo na biyu a bikin kaddamar da sabuwar gwamnati wadda shugaban kasa zai yi a bikin.
Mun kawo jerin rantsar da Shugabannin da aka yi a mulkin Shagari, Obasanjo, ‘Yaradua, Jonathan da Buhari, ganin Bola Tinubu zai karbi ragamar shugabanci a yau.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai miƙa mulki ga zaɓabɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayun 2023. Sabuwar gwamnati ta kafu daga nan.
Ma’aikatar ayyuka na musamman ta fitar da sunayen 'yan siyasa da tsofaffi da Gwamnoni masu-ci da za a ba shaidar girma da Sarakuna da ba su taba samun lambar ba
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Hon. Sha'aban Sharada a matsayin shugaban hukumar kula da almajirai da yaran da basu zuwa makaranta, yana dab da sauka.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da lambar yabo mai muhimmanci ga ministan sadarwa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami bayan kammala aikinsa na ministan kasa.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa bai taɓa tunanin cewa zai zama shugaban ƙasa ba. Shugaban ƙasar mai barin gado ya bayyana hakan ne a Abuja.
Muhammadu Buhari
Samu kari