Mayakan Houthi Sun Yi Bayani kan Zargin kai Hare Hare Makkah

Mayakan Houthi Sun Yi Bayani kan Zargin kai Hare Hare Makkah

  • Mayakan Houthi na Yemen sun musanta zargin kawancen da Saudiyya ke jagoranta na cewa sun harba wani jirgi mara matuki zuwa birnin Makka
  • Wani jami’in kungiyar, Hazem al-Assad, ya ce ikirarin cewa Houthi sun nufi Makka da hari “karya ce tsagoran ta” wadda aka taba amfani da ita a baya
  • Martanin Houthi ya zo ne bayan Saudiyya ta ce ta kakkabo wani jirgi mara matuki da ake zargin kungiyar ta harba zuwa yankin Makka mai alfarma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kungiyar Houthi ta Yemen ta yi watsi da rahoton kawancen da Saudiyya ke jagoranta na cewa kungiyar ta harba jirgi mara matuki zuwa birnin Makka, wuri mafi tsarki ga Musulmi.

Jami’in kungiyar, Hazem al-Assad, ya ce zargin ba shi da tushe, yana mai cewa irin wannan ikirari an taba yin amfani da shi a baya.

Kara karanta wannan

An kai hare hare birnin Makkah, Saudiyya ta dauki matakin gaggawa

Yadda ake ibada a dakin Ka'aba
Mutane na dawafi a dakin Ka'aba da ke Makkah. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Martanin mayakan Houthi

Middle East Eye ta wallafa cewa Al-Assad, wanda mamba ne a ofishin siyasar Houthi, ya ce ikirarin kai hari kan Makka “karya ce da aka dade ana amfani da ita, wadda yanzu ba ta yaudarar kowa.”

Martanin nasa ya biyo bayan zargin kawancen Saudiyya na cewa ya kakkabo wani jirgi mara matuki da kungiyar ta harba zuwa birnin Makka.

Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu bangarorin biyu suna gabatar da bayanai masu sabani kan lamarin.

Kakakin kungiyar Houthi
Mai magana da yawun Houthi, Yahya Saree. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An yi gargadin hari a Saudi

Saudiyya ta fitar da gargadi a ranar Talata kan yiwuwar hare-hare a Makka da wasu yankunan kudancin kasar da ke makwabtaka da Yemen.

Rahoton ND TV ya ce gargadin da aka fitar a Makka shi ne na farko tun bayan barkewar yakin Gabas ta Tsakiya a watan Fabrairu.

Wannan ya zo ne kwana guda bayan wasu hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuki daga Yemen sun raunata mutane 13 a kudancin Saudiyya.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta kunyata Shugaban Amurka bayan ya yi maganar komawa teburin sulhu

Rikicin Yemen ya sake tsananta

Fadan da ke tsakanin Houthi da dakarun gwamnatin Yemen ya sake barkewa a watan Yuli, bayan kungiyar ta kaddamar da wani gagarumin hari kan dakarun gwamnatin kasar.

Mayakan Houthis, wadda suka dade suna da iko da wasu yankunan arewacin Yemen, su kara fadada ayyukan su a cikin sabon rikicin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya tilasta wa mutane 82,000 barin gidajensu tun farkon watan Satumban shekarar 2026..

Batun yakin Iran da Amurka

A wani labarin, kun ji cewa majalisar Wakilan Amurka ta kada kuri’a a karo na 3 kan kudirin kawo karshen yakin Iran, inda ta amince da takaita ikon Shugaba Donald Trump na ci gaba da daukar matakin soji.

Kuri’ar da aka kada a ranar Talata ta kasance 220 a kan 204, inda ‘yan Republican 7 suka hada kai da ‘yan Democrat wajen amincewa da kudirin.

Dan Majalisar Wakilan Amurka daga Iowa, Zach Nunn, ya ce ya goyi bayan kudirin ne saboda a ganinsa, bayan rufe damar tattaunawa, ya kamata kai farmakin soji ya samu amincewar Majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng