Shugaba Buhari Ya Sake Yin Sabon Nadi Yana Dab Da Sauka Kan Mulki

Shugaba Buhari Ya Sake Yin Sabon Nadi Yana Dab Da Sauka Kan Mulki

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sake yin sabon naɗi yana dab da barin madafun ikon ƙasar nan a ranar 29 ga watan Mayu
  • Shugaban ƙasar mai barin gado ya naɗa Sha'aban Sharada a matsayin shugaban sabuwar hukumar kula da almajirai
  • Wannan sabon naɗin ya biyo jerin naɗe-naɗe da shugaban ƙasar ya yi lokacin da ya rage masa saura kaɗan ya yi bankwana da mulki

Abuja - Ƴan sa'o'i kaɗan kafin ya yi bankwana da mulkin Najeriya, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sake yin sabon naɗi.

Shugaba Buhari a ranar Lahadi ya naɗa Sha'aban Sharada a matsayin shugaban hukumar kula da almajirai da yaran da basu zuwa makaranta ta ƙasa, cewar rahoton Premium Times.

Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar da yammacin ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Peter Obi Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Obidients' Da Sauran 'Yan Najeriya

Shugaba Buhari ya yi sabon nadi yana dab da barin ofis
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: Channels Television
Asali: Twitter

Sanarwar na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan sanya hannu da ya yi kan dokar kafa hukumar kula da almajirai da yaran da basu zuwa makaranta ta ƙasa ta shekarar 2023, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin ɗan majalisar tarayya mai barin gado mai wakiltar Kano Municipal, (Dr) Sha’aban Sharada a matsayin shugaba."
Hon. Sharada yana da digiri fannin Mass Communication daga jami'ar Bayero da ke Kano da digirin digir kan Business Administration daga jami'ar Chichester, United Kingdom,”

Shugaba Buhari ya yi naɗe-naɗe yana dab da sauka

Wannan naɗin na baya-bayan nan dai ya biyo bayan irinsa da dama da shugaban ƙasar mai barin gado ya yi lokacin da wa'adin mulkinsa ke dab da zuwa ƙarshe.

Shugaba Buhari a ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023, zai miƙa mulkin ƙasar nan a hannun zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin sabon shugaban Najeriya. Dukkanin su ƴaƴan jam'iyyar APC ne.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Bayyana Muhimmin Abinda Ya Sauya a Najeriya Daga 2015 Zuwa 2023

Shugaba Buhari Ya Karrama Pantami

A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya karrama ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, da lambar yabo ta ƙasa

Shugaban ƙasar ya karrama Sheikh Pantami da lambar yabon ne tare da sauran wasu ministoci da na hannun damansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel