Rikicin APC: Na Hannun Daman Tinubu Ya Gargadi Wike kan Yawan Surutu

Rikicin APC: Na Hannun Daman Tinubu Ya Gargadi Wike kan Yawan Surutu

  • Kakakin kamfen din APC, Ima Niboro ya buƙaci Ministan FCT Nyesom Wike da gwamnonin APC da su daina musayar kalaman da ke nuna suna rikici da juna
  • Ima Niboro ya bayyana rikicin da ke tsakanin Wike da gwamnonin a matsayin 'sabani tsakanin ƴan uwa' inda ya buƙaci su maika hankali kan 2027
  • A bayanin da ya yi shawarce su da su fita zuwa titi, kasuwanni da tsakanin al'umma domin tallata Shugaba Bola Tinubu maimakon yin dogon turanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Ima Niboro, ya buƙaci Nyesom Wike, da gwamnonin APC da su tsakaitar da musayar kalamai a tsakaninsu, su maida hankali wajen kamfen.

Niboro ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba, inda ya kwatanta sabanin da ke tsakanin Wike da gwamnonin a matsayin "rikici tsakanin ƴan uwa".

Kara karanta wannan

Babban Sarki a Najeriya ya fito ya nuna goyon baya ga Tinubu

Nyesom Wike a Abuja
Nyesom Wike na hira da 'yan jarida. Hoto: Lere Olayinka
Source: Twitter

Tashar talabijin ta Arise TV ta ruwaito cewa kalaman nasa sun biyo bayan sukar da Wike ya yi wa gwamnonin APC na kiransu ragwaye a fannin siyasa.

Wike ya caccake su ne bayan sun fito karara sun nuna ba za su hada kai da shi ba domin shiga wata hadaka game da zaben 2027.

Kakakin kamfen din shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa:

"A lokacin da na ce ku rage magana, ban ce ku daina aiki ba. Ku daina magana, ku tafi ku yi aiki. Ku bayyana a gaban kyamarorin talabijin. Ku tafi tsakanin al'umma. Ku tafi hanyoyin titi. Ku tafi kasuwanni. Ku tafi ku shawo kan jama'a."

Batun sukar juna a APC

Tun da farko, Shugaban PGF Hope Uzodimma, ya bayyana cewa gwamnonin APC ba za su goyi bayan wani tsarin siyasar Wike da zai raunana jam'iyyar ko kuma ƙudurin sake zaɓen Tinubu ba.

Kara karanta wannan

2027: Sabon rikici ya barke tsakanin Wike da gwamnonin APC

A kan haka, Ima Niboro ya jaddada cewa kiran da yake yi ba yana nufin wani ɓangare ya mika wuyansa ga wani ba ne, a'a, yana bukatar su nuna karsashinsu ne ta hanyar tattara magoya baya a matakin karkara.

Ya ƙara da cewa:

"Dakatawa da duk wannan dogon turancin da ake yi a ko'ina wanda ba ya kai kowa ko'ina. Ku tafi ku yi aiki. Idan kai shugaban siyasa ne, daina magana. Tafi ka yi aiki. Shi nake bukata."
Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC
Lokacin da gwamnoin APC suka gana da Bola Tinubu a Aso Villa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Martanin gwamnonin ga Wike

A wani labarin daban, kun ji cewa kungiyar gwamnonin APC ya ki yarda da kowani nau'in ƙawance ko tsarin siyasa da zai iya raunana damar sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu ko kuma shafar ƴan takarar jam'iyyar.

Gwamnonin sun bayyana cewa ba za su shiga, goyon baya ko amincewa da wani tsari na siyasa da zai haifar da rabuwar kawuna ko kishiyanta muradun jam'iyya mai mulki ba.

Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya bayyana wannan matsaya ne bayan kammala wani taron sirri da gwamnonin suka yi a masaukin gwamnan jihar Imo da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng