Rantsar Da Bola Tinubu: An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasa A Najeriya Yayin Da Buhari Ya Mika Mulki; Kai Tsaye

Rantsar Da Bola Tinubu: An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasa A Najeriya Yayin Da Buhari Ya Mika Mulki; Kai Tsaye

Wa'adin gwamnatin Asiwaju Ahmed Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 zai fara ne a hukumance bayan rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.

Bikin rantsar da sabon shugaban kasar, wanda kuma zai kawo karshen wa'adin Shugaba Muhammadu Buhari, za a yi shi ne a farfajiyar Eagle Square da ke birnin tarayya Abuja, misalin karfe 10 na safiya.

Za a rantsar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16
Za a yi bikin rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16 a Eagle Sqaure a ranar Litinin 29 ga watan Mayu. Hoto: KOLA SULAIMON/AFP, Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images

Ku kasance tare da Legit.ng Hausa domin samun bayanai kai tsaye kan yadda bikin ke wakana.

An kade-kade da raye-raye a Eagle Square

Bayan rantsar da sabon shugaban kasar, yanzu kuma lokaci ne ga yan Najeriya su baje kolin al'adunsu da wake-wake a filin ta Eagle Square.

Tawagar Wasan Kwaikwayo na kasa za ta yi dirama.

Tinubu ya yi magana

A jawabin farko da ya yi, shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta yi waje da tsarin tallafin man fetur.

Tinubu ya ce ba ayi tanadin kudin tallafin a kasafin kudin shekarar bana, ya ce ana sa ran GDP zai motsa da 6% a shekara.

Buhari ya yi gaba

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bar filin Eagle Square, an rahoto cewa daga nan zai wuce garin Daura a Katsina.

Chris Ngige, Sadiya Faruk, Mohammed Bello da wasu ne suka yi wa tsohon shugaban kasar sallama a filin tashin jirgin sama a Abuja.

Tinubu ya yi rantsuwa

Alkalin Alkalai na kasa, Olukayode Ariwoola GCON ya rantsar da Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya.

Sojoji sun sa sarawa sabon shugaban kasa, hakan ya na zuwa ne bayan Muhammadu Buhari ya mika lambobin girma.

An rantsar da Shettima

Kashim Shettima ya karbi rantsuwa a matsayin mataimakin shugaban kasa. Mai dakinsa, Nana Shettima ta na gefe.

Sanata Kashim Shettima daga jihar Borno ya canji Farfesa Yemi Osinbajo.

Yemi Osinbajo

Kafin karfe 10:00 na safe, Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya iso filin Eagle square da tawagarsa.

Tinubu ya isa Eagle Square

Bidiyo ya tabbatar da cewa Bola Tinubu ya isa filin Eagle Square kafin karfe 10:00 na safe inda za a rantsar da shi.

Da safiyar nan ne zababben shugaban kasar ya bar masaukinsa da ke 'Defense House' a Abuja tare da 'yan tawagarsa.

Bayan halarrar Tinubu, wanda ake jira shi ne mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Kashim Shettima ya iso

Kafin zuwan Bola Tinubu, an sanar da isowar Sanata Kashim Shettima wanda za a rantsar a matsayin mataimakinsa.

Zababben mataimakin shugaban kasar ya shigo filin rantsuwar tare da mai dakinsa da jami'an tsaron da ke kula da shi.

Goodluck Jonathan

Yayin da ake fareti, an ga Goodluck Jonathan tare da mai dakinsa watau Patience Jonathan su na zaune a farfajiyar.

Dr. Goodluck Jonathan ne a mika mulki ga Muhammadu Buhari a irin wannan rana shekaru takwas da suka wuce.

Aliko Dangote a Eagle Square

Attajirin Najeriya watau Aliko Dangote ya na cikin wadanda aka shigowarsu zuwa farfajyar rantsuwar a birnin Abuja.

Wani bidiyo da aka samu daga tashar TVC ya nuna isowar Dangote da Femi Otedola.

Barka da zuwa Ranar Rantsarwa: 29 ga watan Mayu!

Barka da zuwa shafin rahotanni kai tsaye dangane da rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu. Ana gudanar da bikin ne a Eagle Square da ke Abuja, inda a halin yanzu ake cigaba da kintsa wurin.

An yi ruwan sama a safiyar yau, amma ruwan ya tsaya, kuma ana cigaba da shirye-shirye don wannan rana mai cike da tarihi.

An yi bikin cin abinci na rantsarwar

Gabanin rantsar da zababben shugaban kasar, an shirya bikin cin abinci a Aso Rock inda muhimman mutane a kasa da waje suka halarta. Zababben shugaban kasar ya yi jawabi a wurin taron.

Tawagar Wakilan Biden ta iso Abuja don kaddamar da Tinubu

Tawagar mutane tara da aka turo daga Amurka don halartar rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu sun iso Abuja Najeriya a daren jiya.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ce ta tarbi tawagar a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu.

Buhari zai halarci bikin kaddamar da Tinubu?

Ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari da First Lady Aisha Buhari za su halarci bikin rantsarwar.

Akwai yiwuwar shugaban kasar mai barin gado da matarsa su shiga jirgi su shilla zuwa Daura, Jihar Katsina bayan barin Eagle Square.

Tinubu zai yi jawabin rantsarwa?

Ana sa ran Tinubu zai yi jawabin rantsarwa bayan an rantsar da shi. Jawabin zai kunshi wasu kadan daga cikin abubuwan da ake fatan ganin za a aiwatar da gwamnatinsa.

Yadda za a iya kallon bikin rantsar da Tinubu

Yan Najeriya na iya kallon bikin rantsarwar a gidajen talabijin na kasa kai tsaye.

Yan Najeriya da ke kasahen waje za su iya kallo kai tsaye ta shafin Youtube ko wasu tasoshin gida Najeriya.

Legit.ng Hausa ita ma za ta rika kawo rahotanni kai tsaye kan yadda bikin ke gudana.

Rantsar da Bola Tinubu: Wuri da Lokaci

Za a rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ne a filin Eagle Square da ke Abuja. A wurin taron ne aka sa ran Tinubu zai yi rantsuwar kama aiki misalin karfe 10 na safiya.

Amma, baki na musamman da aka gayyata za su fara shiga wurin taron na Eagle Square tun karfe 8 zuwa 8.30 na safe.

Rantsar da sabon shugaban kasar da fareti ga zababben shugaban kasa da zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai fara misalin karfe 10 na safe.

Online view pixel