Rantsar Da Tinubu: Muhimman Abubuwa 3 Da Yakamata Ku Sanya Ido Akai a Ranar 29 Ga Watan Mayu

Rantsar Da Tinubu: Muhimman Abubuwa 3 Da Yakamata Ku Sanya Ido Akai a Ranar 29 Ga Watan Mayu

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023, za a rubuta sabon tarihi a Najeriya, inda za a rantsar da sabon shugaban ƙasa, wanda zai jagoranci ƙasar nan har na shekara huɗu masu zuwa.

A ranar 29 ga watan Mayun 2015, aka rantsar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a matsayin shugaban ƙasa na huɗu tun dawowar ƙasar akan turbar mulkin dimokuraɗiyya.

Buhari zai mika mulki ga Bola Tinubu
Buhari da Osinbajo za su yi bankwana da mulki Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Manyan abubuwan da za su faru a ranar 29 ga watan Mayu

Sai dai, a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023, za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, a matsayin shugaban ƙasa na biyar tun bayan dawowa kan mulkin dimokuraɗiyya, kuma shugaban ƙasa na 16 a tarihin Najeriya.

Kafin zuwan wannan ranar wanda yanzu ya rage ƴan sa'o'i kaɗan, Legit.ng ta tattato jerin abubuwan da za su faru da kuma bukukuwan da ƴan Najeriya yakamata su mayar da hankulansu akai a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Zai Gabatar Da Jawabin Bankwana Ga 'Yan Najeriya, An Bayyana Rana Da Lokaci

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

1. Miƙa mulki

A ranar Litinin 29 ga watan Mayu, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai miƙa mulki a hukumance ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, a dandalin Eagle Square, wajen da za a gudanar da rantsuwa.

Hakan shine zai kawo ƙarshen mulkin Buhari-Osinbajo wanda ya shafe shekara takwas, da kuma farkon sabuwar gwamnati, duk a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC)

2. Rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da mataimakinsa

Za a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, a matsayin sabon shugaban ƙasan Najeriya. Tinubu tare da Shettima za su yi rantsuwar kama aiki, sanann su shirya tunkarar jan aikin da ke gabansu da fara sabuwar gwamnati.

3. Gwamnatin Bola Tinubu ta fara aiki

An samu sabon sarki. Gwamnatin Bola Tinubu za ta fara aiki nan ta ke bayan an kammala rantsuwa. Zai fara daga inda gwamnatin da ta gabace shi ta tsaya.

Kara karanta wannan

"Ku Koma Ofis," Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Lokacin da Zasu Sauka Daga Mulki

Duk da mutane da dama suna sa ran ya kammala haɗa muƙarrabansa, waɗanda za su shiga cikin gwamnatinsa, Tinubu ya yi alƙawarin kafa gwamnati wacce za ta tafi da kowa.

Buhari Ya Ce Tinubu Ne Dan Takara Mafi Cancanta

A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilin da ya sanya Bola Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Shugaba Buhari ya ce Tinubu ya fi sauran ƴan takarar cancanta, sannan ƴan Najeriya ba su yi zaɓen tumun dare ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel