Hanzari Ba Gudu Ba: Kungiyar CNG Ya Bukaci EFCC Ta Hana Duk Na Kusa da Buhari Barin Najeriya

Hanzari Ba Gudu Ba: Kungiyar CNG Ya Bukaci EFCC Ta Hana Duk Na Kusa da Buhari Barin Najeriya

  • Kungiyar CNG ta bukaci hukumar EFCC da kada ta bari wandanda suka rike mukamai a gwamnatin Buhari su bar kasar
  • Kungiyar ta ce yin hakan ne kadai zai tabbatar da adalci a wajen bincike, ba wai kadai tsoffin gwamnoni masu barin gado ba
  • Kakakin kungiyar, Abdul-azeez Suleiman shi ya bayyana haka a yayin taron kungiyar a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya

FCT, Abuja – Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) ta bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da kada su bar wadanda suka rike mukami a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari su bar kasar.

Kungiyar ta na magana ne akan wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa a gwamantin da ta shude musamman gwamnan babban bankin kasar (CBN), Godswill Emefiele akan zargin da ake masa.

Kara karanta wannan

Zargin Kisan Kai: Abba Gida-Gida Ya Sha Alwashin Sake Gurfanar Da Doguwa

Majlisar Zartaswa
Taron Majalisar Zartaswa ta Gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Buhari, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Kakakin Kungiyar, Abdul-azeez Suleiman shi ya bayyana hakan a yayin taron su a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu, inda ta soki masu neman kawo cikas a rantsarwar da aka gudanar jiya a Abuja, cewar Daily Trust.

Kungiyar ta bukaci a hana Emefiele fita waje don karo karatu

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun bukaci a rike duk wadanda suka rike mukami a tsohuwar gwamnati da kada a ba su dama su tsallake Najeriya har sai an tabbatar ba su da wani laifi.
“Musamman gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godswill Emefiele dole ya bayar da bahasi akan abubuwan da ake zarginsa akansu.
“Mun bukaci duk wani mai fita kasashen waje don karo karatu na Emefiele da sauran wadanda suka rike mukamai, a rushe su har sai an gama bincike don samun gwamnatin adalci.”

Kungiyar ta zargi hukumar da nuna wariya a bincikenta

Kara karanta wannan

A banza: Peter Obi ya fadi abin da zai faru dashi bayan an rantsar da Tinubu

Kungiyar ta bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da su kara bincike akan badakalar da ake yi a ma’aikatu da sauran hukumomi na gwamnati don gurfanar da masu laifi.

Kungiyar ta kara da cewa:

“Mun yi Allah wadai da yadda ake binciken iya gwamnoni masu barin gado, muna kira ga shugaban EFCC ya fadada bincikensa zuwa fadar shugaban kasa da ma’aikatun gwamnatin tarayya da kuma masu mulkin siyasa a tsohuwar gwamanti ta Buhari.
“Kuma muna kira a binciki ita kanta hukumar EFCC don adalci, hakan zai rage yawan basukan da gwamnatin Buhari ta ci ga kasar Najeriya.”

Gwamna Ortom Ya Yi Martani Kan Rahoton Shirin EFCC Na Kama Shi

A wani labarin, Gwamna Samuel Ortom ya yi martani akan rahoton da ake yadawa cewa hukumar EFCC na shirin kama shi.

Hadimin yada labaran tsohon gwamnan, Terver Akase shi ya karyata wannan rahoto a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel