Minista Pantami Ya Ciri Tuta, Buhari Ya Karrama Shi da Lambar Yabo Mai Muhimmanci

Minista Pantami Ya Ciri Tuta, Buhari Ya Karrama Shi da Lambar Yabo Mai Muhimmanci

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu tare da ba minista Pantami lambar yabo ta CON gabanin barin mulki
  • Hakazalika, an ba da irin wannan lambar yabo ga minista Sadiya Umar Farouq, ministar jin kai da walwala
  • Za a rantsar da Bola Tinubu a ranar Litinin, ana ci gaba da hango kujerun da za a raba nan take bayan karbar Buhari

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da lambar yabo ga wasu daidaikun manyan na hannun damansa a gwamnatinsa da ta ke dab da shudewa.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami na daya daga cikin wadanda suka samu lambar yabon CON.

Wannan na fitowa ne daga bakin ministan a cikin wata sanarwar da ya yada a kafar sada zumunta ta Twitter Lahadi, 28 Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

A banza: Peter Obi ya fadi abin da zai faru dashi bayan an rantsar da Tinubu

An karrama Pantami da lambar yabo mai kyau
Ministan Sadarwa mai barin gado, Sheikh Pantami | Hoto: Prof. Isa Ali Ibrahim
Asali: Twitter

Abin da yasa Buhari ya karrama su Pantami

Da yake bayyana yabon da shugaban ya ba shi, ministan ya ce Buhari ya yi la’akari ne da irin kokarin da ya yi tare da tagwarorinsa na tsawon lokaci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

“Yanzun nan na samu labari mai dadi cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCON ya yaba da nasarorin da muka samu ta hanyar ba da babbar lambar yabo ta kasa wato Commander of the Order of the Niger (CON) a gare ni. Godiya mai yawa, Shugaban FRN! Godiya mai ‘yan Najeriya.”

An ba Sadiya Farouq lambar yabo

Baya ga Minista Pantami, shugaban kasar ya kuma ba da irin wannan lambar yabo ga ministar jin kai da walwala ta kasa, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

A cewar Buhari, ya yaba da irin kokarin da ministocin suka yi wajen tabbatarwa da dogewa kan manufofin gwamnatinsa na kawo ci gaba ga kasa.

Kara karanta wannan

Bankwana: Buhari ya ba Sadiya Farouq lambar yabo saboda yadda take tausayin 'yan Najeriya

Ba wannan ne karon farko da Buhari yake karramawa wasu masu fada a ji da kuma wadanda suka ba da gudunmawa ba ga Najeriya.

Za a rantsar da Tinubu, akwai yiwuwar ya yi sabbin nade-nade

Yayin da mulkkin Buhari ya zo karshe, ana ci gaba da bayyana hasashen wadanda ka iya samun kujeru a mulkin Bola Ahmad Tinubu.

A cewar majiya, akwai mukamai huda uku da sabon shugaban kasar zai ba da nan take bayan karbar mulki daga hannun Buhari.

An naqalto cewa, mukaman kakakin shugaban kasa, shugaban ma’aikata da sakataren gidan gwamnati ne ake sa ran Tinubu zai nada nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel