Ana Rigimar Wike da Gwamnonin APC kan Tinubu, Shettima Ya Fasa Kwai kan Zaben 2023

Ana Rigimar Wike da Gwamnonin APC kan Tinubu, Shettima Ya Fasa Kwai kan Zaben 2023

  • Kashim Shettima ya bayyana gwamnonin jihohin Arewa da suka goyi bayan Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
  • Ya ce Tinubu bai bari rashin goyon bayan wasu gwamnoni ya hana shi ci gaba da neman shugabancin Najeriya ba
  • Shettima ya yi kira ga ’yan siyasa da su sasanta bayan fafatawar zaɓe, yana cewa sabanin siyasa bai kamata ya zama dalilin ƙiyayya ta dindindin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kwara - Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnoni shida kacal daga cikin jihohin Arewa 19 ne suka goyi bayan takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Shettima ya ce duk da rashin goyon bayan wasu daga cikin gwamnonin, Tinubu bai bari hakan ya hana shi ci gaba da neman shugabancin ƙasar ba.

Kara karanta wannan

Babban Sarki a Najeriya ya fito ya nuna goyon baya ga Tinubu

Shettima ya yi magana kan Tinubu
Kashim Shettima na gaisawa da Shugaba Tinubu Hoto: @stanley_nkwocha
Source: Facebook

Shettima ya yi magana a Ilorin

Jaridar Daily Trust ta ce Shettima ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 16 ga watan Satumban 2026 a fadar Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, yayin bikin naɗa Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a matsayin Sardaunan Masarautar Ilorin.

Ya ce yanayin siyasar da ya dabaibaye zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya kasance cike da tsananin fafatawa.

A cewarsa, an samu matsaloli da dama da suka tasowa Tinubu, amma hakan bai sa ya hakura da burinsa ba.

“Dukkanku kun san cewa muna da jihohi 19 a Arewa. Daga cikin waɗannan, shida ne kacal suka yarda da Tinubu kuma suka goyi bayansa, amma Tinubu bai bari hakan ya hana shi ba. Ya iya tsallake wannan kalubale,” in ji Shettima.

Ya yi kira ga ’yan siyasa su sasanta

Shettima ya ce abin da ya faru a zaɓen 2023 ya kamata ya zama darasi ga ’yan siyasar da ke shirin fafatawa a zaɓuka na gaba.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya fadi dalilin da ya sa Arewa ba za ta juyawa Tinubu baya ba a 2027

Ya jaddada cewa bambance-bambancen siyasa bai kamata su rikide zuwa rarrabuwar kai ta dindindin tsakanin ’yan siyasa masu neman mukaman zaɓe ba.

Musamman ma, ya yi kira ga ’yan siyasar Kwara da su sasanta bayan kammala zaɓen fidda gwani na All Progressives Congress (APC), ba tare da la’akari da wanda ya samu nasara ba.

Ya ce bai kamata a ɗauki fafatawar siyasa a matsayin yaƙin da tsofaffin abokan hulɗa za su koma maƙiya na har abada ba.

Ya ce Tinubu ya yafewa gwamnoni

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce Tinubu ya nuna irin wannan hali bayan zaɓen 2023, lokacin da ya nemi sulhu da wasu gwamnoni daga Arewa waɗanda ba su goyi bayan takararsa ba.

“Bayan zaɓen 2023, Shugaba Tinubu ya rungumi tare da yafewa duk sauran gwamnoni daga Arewa waɗanda ba su goyi bayansa ba. Wannan alama ce ta shugaba nagari,” in ji shi.
Shettima ya yi magana kan zaben 2023
Kashim Shettima na addu'a a wajen taro Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Shettima ya yabi Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cancanci yabo maimakon suka saboda sauye-sauyen tattalin arziki da ta aiwatar.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a fannin tattalin arziki sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng