Jonathan Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ministocinsa, Da Masu Muƙami Suka Ji Tsoron Buhari a 2015

Jonathan Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ministocinsa, Da Masu Muƙami Suka Ji Tsoron Buhari a 2015

  • Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana dalilin da ya sanya ministocinsa da sauran masu muƙami suka tsorata da Buhari a 2015
  • Ya ce sunyi tunanin cewa da Buhari ya karɓi mulki zai tura su zuwa gidan yari ba tare da jin ta bakunansu ba
  • Jonathan ya yi kira ga masu riƙe da muƙaman siyasa kan su riƙa sanya Najeriya a farko kafin buƙatunsu na ƙashin kansu

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ministocinsa sun yi fargabar cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tura su gidan yari ba tare da ko jin ta bakinsu ba.

A cikin rahoton Daily Trust, Jonathan ya bayyana cewa wasu daga cikin ministocin da suka yi aiki da shi sun firgita a lokacin da Buhari ya karɓi mulki suna tunanin zai tsaurara musu.

Jonathan ya bayyana dalilinsa na amincewa da sakamakon zabe
Jonathan ya ce mukarrabansa sun firgita da Buhari a 2015. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Jonathan ya bayyana hakan ne yayin a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, inda ya ce wasu daga cikin ministocinsa ma suna ganin cewa zai gudu, amma sai ya zauna a kasar.

Jonathan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A lokacin mulkina musamman lokacin zaɓen 2015, ministocina, manyan jami’ai, waɗanda suka yi aiki tare da ni; sun riƙa fargabar cewa mun fadi zabe, mecece makomarmu?”
“Shin sabuwar gwamnati za ta tura mu gidan kurkuku ba tare da jin ta bakinmu ba? Domin gwamnati ta na gaba da kotu kuma tana iya yanke hukuncin da ta ga dama."

Jonathan ya bayyana dalilin da ya sa ya amince da shan kaye

Jonathan ya kuma ce irin halin tashin hankalin da muƙarrabansa suka shiga a lokacin miƙa mulki a 2015, muƙarraban Buhari ba su fuskanci irinsa ba.

Da yake ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya amince da shan kaye a hannun Buhari, ya ce ƙasar ce a gabansa fiye da kansa.

A rahoton The Punch, Jonathan ya ƙara da cewa yana da kyau masu rike da muƙaman siyasa su fi son ƙasar nan fiye da kansu, yana mai cewa idan babu ƙasar, to ba za a samu shugaban ƙasa ba.

Jonathan ya shawarci hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC)

Jonathan ya kuma ce, duk da sauya tsarin zaɓen da aka yi zuwa amfani da na'ura, har yanzu akwai ƙalubale a gaban hukumar zaɓe.

Ya yi gargadin cewa dole ne hukumar zabe ta ƙasa (INEC) ta natsu ta duba abubuwan da kyau, idan ba haka ba kuma wata rana za ta jefa kasar nan cikin tashin hankali.

Buhari ya sanar da wasu sabbin muƙamai ana kan rantsar da Tinubu

A wani labarin namu na baya, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanar da wasu sabbin muƙamai ana tsaka da bikin rantsar da sabon shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Sanarwar dai wacce hadimin tsohon shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, ta iso hannun gidajen watsa labarai ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar jiya Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel