Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Ta'adda Sama da 1000 a Jiha 1 da ke Arewacin Najeriya

Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Ta'adda Sama da 1000 a Jiha 1 da ke Arewacin Najeriya

  • Dakarun Operation Hadin Kai sun hallaka ’yan Boko Haram da ISWAP 1,106 tare da cafke sama da N300m na kuɗaɗen haram daga masu ɗaukar nauyinsu
  • Sojojin sun cafke aƙalla mutane 758 da ke taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’addan wajen samar da kayan aiki da sauran buƙatunsu
  • Fiye da mayakan JAS/ISWAP 969 da iyalansu sun miƙa wuya a cikin shekarar da ta gabata sakamakon matsin lambar soji da tattaunawar sulhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Maiduguri - Dakarun rundunar sojoji ta Operation Hadin Kai (OPHK) sun hallaka ’yan Boko Haram da ISWAP 1,106 tare da kwace fiye da N300m na kuɗaɗen haram da ke da alaka da yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Boye boye ya kare, Amurka ta bayyana gagarumar barnar da Iran ta yi mata

Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai mai barin gado, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin jawabinsa na bankwana da aka gudanar a Maiduguri, Jihar Borno.

Operation Hadin Kai.
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai mai barin gado, Manjo Janar A.E Abubakar Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Rundunar sojojin Najeriya ta wallafa sanarwar nasaorin da kwamanda mai barin gado ya samu a Operation Hadin Kai a shafinta na Facebook.

Sojoji sun cafke masu taimaka musu

A cewar kwamandan mai barin gado, manyan ayyukan sojin sun kuma kai ga cafke mutane 758 da ke taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’addan wajen samar musu da kayan aiki.

Ya ce sojojin sun kwato makamai iri daban-daban sama da 475 da kuma harsasai 24,409 masu nau’o’i daban-daban.

“An kuma gano na’urorin fashewa watai bama-bsmai kirar cikin gida (IEDs) guda 295, inda aka tarwatsa su cikin aminci,” in ji shi.

Ya danganta nasarorin da aka samu da haɗa matsin lambar soji mai ɗorewa da kuma ingantattun hanyoyin hulɗa da al’umma da sauran matakan da ba na yaƙi ba.

Mayakan ISWAP sun miƙa wuya

Kwamandan ya ce wannan salon aiki guda biyu ya haifar da yawan mayakan da suka miƙa wuya fiye da kowane lokaci, inda sama da mayakan JAS/ISWAP 969 da iyalansu suka ajiye makamansu cikin shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai kazamin harin da ya jawo asarar rayuka da kona gidaje

Ya kuma ce samu manyan nasarori wajen ceto mutanen da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.

“An ceto fararen hula 638 daga sansanonin ’yan ta’adda, sannan an samu nasarar ceto dukkan ɗalibai 46 a yayin yunƙurin sace su a makarantar kwalejin mata ta Monguno, da sauran ayyuka,” in ji shi.
Sojoji.
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai suna faretin bankwana da tsohon kwamandansu a Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

An kashe manyan kwamandoji

Ya ce daga cikin fitattun shugabannin ’yan ta'addan da aka lashe a karkashinsa akwai Abu Bilal Al-Muniki (Abu Mainok), da Malam Jidda (Amir na ƙauyukan Ngorgore/Malumti).

Sauran sun hada da Abu Modu, Modu Dogo, Munzir na Dogon Chukun, Abu Aisha (Qaid na Tumbun Mota), da Abul Kaka, da sauran su.

Ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba shi ta yi wa ƙasa hidima, da kuma Gwamnatin Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da dama sun mutu da suka gamu da bala'in da ya fi ƙarfinsu a daji

An nada sabon kwamandan Operation Hadin Kai

Kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta naɗa sabon kwamandan Operation Hadin Kai, inda ya maye gurbin Manjo Janar Abdulsalam Abubakar.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Kanal Appolonia Anele ta bayyana sauyin ne cikin wata sanarwa ranar Laraba, 9 ga watan Satumban 2026.

Sabon kwamandan , Manjo Janar Ibikunle Ademola Ajose, ya maye gurbin Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, wanda shi ne kwamanda na 15 na Operation Hadin Kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262