"Ban Taba Tunanin Cewa Zan Shugabanci Najeriya Ba", Shugaba Buhari

"Ban Taba Tunanin Cewa Zan Shugabanci Najeriya Ba", Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ɓai tunanin cewa zai mulki Najeriya ba
  • Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin yara manyan gobe a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa
  • Shugaban ƙasar na ci gaba da yin bankwana da mulkin ƙasar nan, inda zai miƙa mulki ranar Litinin, 29 ga watan Mayu

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai taɓa sanin cewa zai shugabanci ƙasar nan ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Garba Shehu, ya fitar, shugaba Buhari ya ce bai taɓa tunanin zai shugabanci ƙasar nan ba a matsayin soja sannan a matsayin farar hula, cewar rahoton Daily Trust.

Shugaba Buhari ya ce bai taɓa tunanin zama shugaban kasa ba
Shugaba Buhari tare da yara manyan gobe Hoto: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu yara ɗalibai daga wasu makarantu na birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Peter Obi Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Obidients' Da Sauran 'Yan Najeriya

Buhari ya shawarci yaran da su gina Najeriya wacce za su yi alfahari da ita, ta hanyar gaskiya, kishin ƙasa da haɗin kai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙarfafa guiwoyinsu kan su zama ƴan ƙasa nagari kafin su zama shugabanni, inda ya nuna muhimmanci kan dogaro da kai da nauyin ginawa da ciyar da ƙasar nan gaba ya ke da shi.

A kalamansa:

"Allah maɗaukakin sarki ya bani aron rayuwa na girma daga yaro zuwa babba. Lokacin muna ɗalibai, an gaya mana cewa mu ne shugabannin gobe. Ɓan taɓa sanin cewa wata rana zan shugabanci ƙasa ta ba, ballantana har na jagorance ta sau biyu a matsayin soja da farar hula.
"Saboda haka, ina so na gaya mu ku cewa a cikin ku akwai kansiloli, ƴan majalisu, gwamnoni da shugabannin ƙasa. Amma dole sai kun zama ƴan ƙasa nagaru kafin ku zama shugabanni.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Bayyana Muhimmin Abinda Ya Sauya a Najeriya Daga 2015 Zuwa 2023

"Za ku iya zama injiniyoyi, likitoci, ƴan jarida, masana kwamfuta, alƙalai, lauyoyi da sauransu. Wata rana ƙasar nan hannun ku za ta koma. Ba zamu shigo da wasu daga ƙasar waje su zo su tafiyar mana da ƙasa ba. Dole mu da kan mu za mu yi hakan."

Shugaba Buhari zai yi bankwana da mulki

Wa'adin mulkin shugaba Buhari na shekara takwas, wanda ya fara a ranar 29 ga watan Mayun 2015, zai zo ƙarshe a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Ya shugabanci ƙasar nan a mulkin soja daga ranar 31 ga watan Disamban 1983 zuwa ranar 27 ga watan Agustan 1985, bayan ya hamɓarar da gwamnati mai ci ta Shehu Shagari.

Buhari Zai Yi Jawabin Bankwana

A wani rahoto na daban kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabinsa na bankwana ga ƴan Najeriya.

Shugaban ƙasar mai barin gado zai gabatar da jawabin ne yayin da wa'adin mulkinsa ya rage saura ƴan sa'o'i kaɗan.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Yi Kira Mai Daukar Hankali Ga Atiku Da Peter Obi a Jawabin Bankwana

Asali: Legit.ng

Online view pixel